Hatsarin mota ya yi ajalin wani mutum a kan titin Oshodi, a jihar Legas.
Hadarin ya faru ne sakamakon tsinkewar birkin babbar motar kirar bas, wadda ta yi kan daya motar ta murkushe ta a safiyar Juma’a.
- Yadda kudin fansa ya fallasa matashin da ya sace budurwa
- 6 ga Mayu ne sabon wa’adin hada lambar waya da NIN
- Jini ta hanci ta baki ya rika zuba bayan yi wa wata mata rigakafin Coronavirus a Kaduna
- Mai larurar tabin hankali ya tashi hankalin masu ibada a Masallacin Harami
Hukumar Agajin Gaggawa ta Jihar Legas (LASEMA), ta isa wajen don kai dauki ga wadanda hadarin ya ritsa da su.
LASEMA ta bayyana cewa mutum daya ya rasa ransa, sannan biyu sun samu raunuka daban-daban kuma jami’an hukumar, sun kai su wani asibiti a yankin na Oshodi.
Wanda ya rasa ransa kuma an ajiye gawarsa a asibitin, kafin ’yan uwansa su dauki gawar.