✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutanen Sabon Birni na gudun hijira a Nijar

Mazauna garuruwa 14 ga Jihar Sakkwato sun tsere zuwa Jamhuriyar Nijar domin samun mafaka bayan ’yan bindiga sun tarwatsa kauyukansu. Aminiya ta gano a cikin…

Mazauna garuruwa 14 ga Jihar Sakkwato sun tsere zuwa Jamhuriyar Nijar domin samun mafaka bayan ’yan bindiga sun tarwatsa kauyukansu.

Aminiya ta gano a cikin mako guda ’yan bindiga suka tafkata ta’asar tare da kashe mutum 15 a kauyukan da ke Karamar Hukumar Sabon Birni ta Jihar Sakkwato.

Yankin Sabon Birni ya shafe shekaru yana fama da hare-haren ’yan bindiga, lamarin da ya sa wasu mazauna tserewa zuwa Jamhuriyar Nijar domin tsira da rayuwarsu.

Tsohon Shugaban Karamar Hukumar, Idris Gobir, ya ce maharan sun kashe akalla mutum 10 sannan suka sace dabbobi sama da guda 1,000.

“Ba za ka samu ko mutum daya a kauyukan ba, yawancinsu sun tsere zuwa Jamhuriyar Nijar suna gudun hijira,” inji shi.

Kauyukan da maharan suka far wa su ne: Garin Abara, Ungwuar Abzin, Garin Namaimai, Garin Amadu da Garin Danjari; Sauran  Garin Buta, Kalage, Kaihin Aska, Rukkumi da kuma Garin Dubu, Kyara Naguliya, Garin Buka da Kyalkyale.

Shi ma wani mazaunin Sabon Birnin, ya ce a cikin mako biyun da suka wuce an kashe mutum 12 a yankin.

Wakilinmu ya gano an harbi mutum biyar a kauyen Tsamaye, amma daya ne a cikinsu ya rasu, sauran ana jinyar su a asibiti; A ranar Asabar kuma an kashe mutum uku a kauyen Kurawa da dare.

Kafin nan, ranar Juma’ar makon jiya an kashe mutum uku a kauyen Dangari da wasu ku a Kalage a ranar Laraba.

A kauyukna Zurudu da Garin Idi an kashe mutum daya-daya, aka kuma raunata wani, wanda a yanzu yake samun kula a asibiti a Jamhuriyar Nijar.

Ko a ranar Lahadi sai da aka kashe mutum uku a wani harin ’yan bindiga a Garin Hullo da Tarah.

Sun kuma tilasta wa kauyen Makuwana biyan harajin Naira miliyan 10 domin kar a kai musu hari.

Da yake tabbatar da hare-haren, kwamishinan tsaron Jihar Sakkwato, Garba Moyi ya ce ana kai hare-haren ne a yankin Tangaza da Illela da wasu sassan jihar.

“Mutane na kiran jami’an tsaro amma ba sa kawo musu dauki, musamman sojoji; Sun ce yawancin hare-haren, ana kai musu ne bayan sojoji sun shigo yankunan sun nuna karfinsu,” inji kwamishinan.

Amma kakakin Runduna ta 8 ta Sojin Kasan Najeriya, Manjo Adamu Yahaya ya musanta zagin, domin a cewarsa, koyaushe sojoji na hanzarin kai dauki idan suka samu kira.

“Babban Kwamandan Rundunar (GOC) ya umarci sojoji su gaggauta kai dauki idan aka kira su, su kuma tabbata sun kubutar da mutanen da aka yi garkuwa da su.

“Ko a makon jiya sai da Kwamandan Birged na soja ya jagoranci wani shara a yankin,” inji shi.

Ya karyata labarin da ke yawo cewa an janye sojoji a yankin, yana mai cewa, “Gaskiyar magana ita ce, Babban Hafsan Sojin Kasa ya tura da karin sojoji.”