✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutanen Moroko sun yi rub-da-cikin ta’aziyyar dan Siriya da ruwa ya ci

dimbin mutane a kasar Moroko sun tattaru a gabar kogin kasar don yin ta’aziyyar wani yaro dan shekara uku, mai suna Aylan Kurdi dan kasar…

dimbin mutane a kasar Moroko sun tattaru a gabar kogin kasar don yin ta’aziyyar wani yaro dan shekara uku, mai suna Aylan Kurdi dan kasar Siriya da ya nutse a ruwa, inda daga bisani aka watso shi waje a rub-da-ciki. Masu ta’aziyyar sun rika yin rub-da-ciki a gabar ruwan da ke babban birnin kasar Rabat.
Kafafen watsa labarai da shafukan sadarwa na intanet sun nuna hoton Aylan Kurdi a ringingine a kan wani tarin kasa da ake kira Bodrum, a wani wurin shakatawar ’yan yawon bude-ido da aka yi wa lakabin Firayiministan Turkiyya.