✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutanen gari sun kone ’yan bindiga a Kaduna

Mutanen gari sun kone gawar wasu da ake zargin ’yan bindiga ne a yankin Nasarawa-Azzara da ke Ƙaramar Hukumar Kachia da ke Jihar Kaduna

Mutanen gari sun kone gawar wasu da ake zargin ’yan bindiga ne a yankin Nasarawa-Azzara da ke Ƙaramar Hukumar Kachia da ke Jihar Kaduna.

Wani shugaban yankin ya shaida wa wakilinmu ranar Lahadi cewa mutanen garin sun tsinci gawar ’yan bindigar ne a Hayin-Dam da ke kusa da su garin nasu.

Wani ɗan banga mai suna Hassan, ya ce bayan gano gawarwakin ne matasan garin suka banka musu wuta, kafin isowar ’yan banga.

Hakan na zuwa ne bayan rahotanni sun nuna cewa a ranar Laraba sojoji sun kashe wasu ’yan bindiga uku a ƙauyen Azzara da ke maƙwabtaka da yankin na Nasarawa-Azzara.

Wakilinmu ya yi kokarin ganawa da kakakin ’yan sanda na Jihar Kaduna, ASP Hassan Mansur, kan lamarin, amma ya kasa samun jami’in.