Kawo yanzu adadin mamatan da girgizar kasa ta zama silar ajalinsu a kasar Morocco sun zarta 2,800 a yayin da kwarin gwiwar samo karin mutane a karkashin baraguzai ke ci gaba da ja baya.
Alkaluma sun tabbatar da cewa wannan ita ce girgizar kasa mafi muni da kasar ta taba gani a tarihin ta, la’akari da yawan mutanen da suka mutu da kuma dubbai da suka jikkata.
Sa’o’i 48 bayan faruwar ta, ana fargabar samun masu rai a karkashin kasa zai yi wuya, duba da yadda aikin ceton ke tafiyar hawainiya.
Kafar talabijin din kasar ta tabbatar da mutuwar mutane 2,862, sai wasu 2,562 da suka gamu da munanan raunuka.
Masu aikin ceto na kasashen duniya da suka isa kasar sun koka da yadda laka ke hana aikin sauri.
Tawagar masu aikin ceton daga kasashen Spaniya, Burtaniya da kuma Qatar ne suka hallara don taimaka wa takwarorinsu na Morocco, a dai-dai lokacin da ake fargabar da wuya a kara samo masu rai a kasa, saboda yadda lokaci ke dada yin nisa.
Bayanai sun ce wadanda suka tsira daga girgizar kasar sun shafe kwanaki uku yanzu haka a waje, saboda yadda girgizar kasar ta lalata gidajen su.
Faya-fayan bidiyon da ke yawo a kafafen sada zumunta sun nuna yadda mata da kananan yara ke samun mafaka a tantunan wucin gadi da aka kafa a filin Allah ta’ala, yayin da maza ke rayuwa ba tare da tantin ba.
Sai dai jama’a a kasar na ci gaba da kokawa kan yadda ceton ke tafiyar hawainiya, kamar yadda Hamid Ben Henna mazaunin kauyen Tafeghaghte, na gabashin kasar da ya rasa dansa mai shekaru 8, ya ce har kawo yanzu ba’a kai ga ceto dan sa mai shekaru 3 da gini ya danne ba, a don haka suna cikin fargaba da rashin tabbas.