Ga wasu mutum uku daga cikin wadanda kafar Facebook ta sauya rayuwarsu ta kyakkyawar fuska a cikin dan kankanin lokaci.
Facebook kafar sa da zumunta ce ta zamani inda ake haduwa ana tattauna batutuwa da dama, sannan ake nishadi da sauransu; Wasu suna ganin kafar a matsayin wurin badala, wasu kuma na daukar ta a matsayin wajen kasuwanci, wasu kuma suke karatu da sauransu.
- An cafke masu garkuwa da dailiban Bethel Baptist
- Ba za mu fallasa masu taimakon ’yan ta’adda ba —Gwamnati
A wani bincike da Aminiya ta yi, ta gano cewa ana amfani da Facebook wajen sauya rayuwar mutane da dama.
A kwanan nan, wani dalibi da aka ga hotonsa a Facebook a kan keke yana tafiya makaranta a cikin ruwa har ya jawo hankalin mutane ya samu tallafin mutane.
Malam Ibrahim Sanyi-Sanyi ne ya fara maganar, inda ya sanya hoton dalibin a ranar 3 ga Satumba, 2021 sannan ya ce, “Don Allah duk wanda ya san dalibin nan ko makarantarsa, ya sanar da mu. Za mu sama masa rigar ruwa da sauran tallafin da zai kara masa karfin gwiwa da azamar karatu.”
An yi ta yin tsokaci a a kasan rubutun, sannan an yada shi sau 625.
Daga cikin masu tsaokacin akwai wadanda suka ce Makaranar GSS Sabuwar Kofa ce a Kano.
Wani mai suna Haladu Musa Mohammed kuma ya ce, “Akwai wani bawan Allah da ya ce ya gane bajin. Makarantar a Potiskum ta ke, shi ma ya yi makatantar, zai tura wa Principal hoton ya binciko shi.”
A ranar 8 ga Satumba, Malam Ibrahim Sanyi-Sanyi ya sake tuni, inda ya ce, “Mun samu hoto da ya fi fitowa fili. Muna godiya ga Muhammad Balarabe Hussein da Bappancey Eys Eym. Har yanzu muna ci gaba da neman dalibin.”
Sai a ranar 18 ga Satumba ne aka samu damar gano dalibin, inda Malam Ibrahim ya sanya hotonsa, sannan ya rubuta cewa, “A karshe mun gano dalibin mai suna Malam M (an boye sunansa).
“Dalibin aji daya ne a babbar sakandire ta Government Arabic Secondary School, Kura. Yana tuka keke daga kauyen Kwarkyan da ke Karamar Hukumar Garun Malam komai ruwa ko rana zuwa makaranta.
“Muna godiya ga Malam Muhammad Balarabe Hussein Kura wajen gano wannan dalibin.”
Malam Ibrahim ya kara da cewa, “Dalibin yana bukatar tallafi. Zan ba shi tallafin kayakin karatu da rigar ruwa da jakar makaranta da sauran abubua na Naira dubu 100. Kofa a bude take na taimakon sa.”
Nan take aka fara bayyana tallafin da za a ba dalibin, wasu na kudi, wasu kuma na kayan karatu daban-daban.
A ranar 20 ga Satumba ce Malam Ibrahim ya sanya bayanin kudaden da aka samu da sauran tallafin kamar haka:
- Dr. Abdulrazak N10,000
- Dr. Adamu N10,000
- ISS N100,000
- Malam Salisu N20,000
- Malam Ibrahim Imam Ikara N1,000
- Malam Salisu N20,000
- Bello Bature Karfi N3,000
- Dr. A N40,000 (sannan ya yi alkawarin kara kudi domin biyan kudin makarantar dalibin)
Jumulla: N204,000
– Magajiya Dambatta
Idan ba a manta ba, Aminiya ta ruwaito yadda fitaccen dan jarida Jafar Jafar ya yi amfani da Facebook wajen mayar da tsohuwar mawakiya Magajiya Dambatta miloniya daga mabaraciya.
Magajiya Dambatta, wadda asalin sunanta Halima Malam Lasan, an haife ta ce kimanin shekara 84 da suka gabata, kuma ta yi tashe da shahara sosai, inda ta kasance cikin mawaka manya da duniyar Hausa ke sauraro kuma suka yi takama da su a tsakanin shekarun 1970 zuwa 1980.
Bayan dogon lokaci tana tashe, sai kwatsam ta yi batar dabo, inda aka daina jin duriyarta, wadanda suka san ta kuma suka manta da ita, matasa kuma da ma can ba su santa ba.
Da baya sai kawai ganin ta aka yi a wani kauye tana yawon bara.
A nan ne Jafar Jafar ya je ya same ta, ya yi hira da ita sannan ya sanya a Facebook, inda aka tara kudi, aka kai ta asibiti aka yi mata aikin ido, aka gina mata katafaren gida, sannan aka ware kudade da za a rika ba ta domin cin abinci da duba lafiyarta na twason lokaci.
– Mai jarin N100 ya bude shagon kansa a kwana 10
A wani labari na daban, wani karamin yaro ne da ya fara kasuwanci kamar wasa a cikin kwali da kayan da ba su kai Naira 100 ya zama cikakken dan tireda a kwana 10.
Kimanin mako biyu da fara kasuwancinsa a cikin kwalnin ne kafafen sada zumunta suka cika da hotunan yaron.
A lokacin, hotunan sun nuna yaron ne a zaune da ya kasa kayansa a cikin wani kwali a matsayin shago, ya zuba kayan tireda na Naira 100 a ciki da nufin sayarwa a garin Rano da ke Jihar Kano.
Hakan ya jawo wa yaron mai suna Isma’il daukaka, inda bayan an yi ta yada hotunansa, aka rika samun wadansu suna kai masa tallafi.
Daga cikin wadanda suka tallafa masa akwai Malam Ibrahim Yala, wanda ake yi lakabi da Mai Bakandamiyar Buhari, inda ya yi takanas ta Kano daga Jihar Kaduna ya je ya tallafa wa yaron.
Hakan ya sa shagon ya canja hattar rayuwar mahaifin yaron.