✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mutanen da aka kashe a Katsina sun karu zuwa 84

Jami’an tsaro da ’yan sa-kai sun gano karin gawarwaki 26 bayan 58 na farko a yankin Bakori

Adadin mutanen da ’yan bindiga suka kashe a kananan hukumomin Bakori da Kankara na Jihar Katsina ya karu daga 58  zuwa 84.

A ranar Asabar da yamma ne jami’an tsaro da ’yan sa-kai suka gano karin gawarwaki 26 bayan 58 na farko a yankin Bakori da ’yan bindiga suka kai wa mutanen harin kwanton bauna.

Wani ganau a kauyen ’Yargoje ya shaida wa Aminiya cewa ya ga motocin jami’an tsaro sun dauko gawarwaki akalla 26, za su kai yankunan Bakori.

A ranar Juma’a Aminiya ta kawo rahoton cewa a yammacin Alhamis ’yan bindiga sun kashe mutum 41 tare da jikkata wasu da dama, ciki har da ’yan banga da wasu mutanen gari a yankin Bakokri-Ka kara.

Sun kuma bayyana cewa akwai yiwuwar karuwar adadin idan aka bincika cikin dajin da aka yi musu kwanton bauna.

Ajali ya ritsa da ’yan bangar da saurab mutanen garin ne a hanyarsu ta kai wa ’yan bindigar hari da nufin kwato shanun da bata-garin suka sace daga Bakori.

Ba su sani ba ashe ’yan bindigar na da labari, inda suka yi kwanton bauna a cikin daji suka bude musu wuta.

Mashawarcin Gwamna Aminu Bello Masari kan Sah’anin Tsaro, Ibrahim Ahmed-Katsina, ya ce gwamnatin za ta kafa kwamitin bincike domin gano musabbabin abin da ya faru domin daukar matakin da ya dace.

A cewarsa, gwamnatin ta yi alkawarin bayar da tallafi ga mutanen da abin ya shafa.

Mun tuntubi kakakin Rundunar ’Yan Sanda na Jihar Katsina, SP, Gambo Isah, amma ya ce ba shi da labari tukuna.