✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutanen banza da azzalumai ke kawo rikici a Kannywood – Sunusi Oscar

Sunusi Oscar 442 fitaccen darakta ne da ke jan zarensa a Kannywood, musamman yadda masu kallon fina-finan Hausa suke son kallon fina-finansa. A tattaunawarsa da…

Sunusi Oscar 442 fitaccen darakta ne da ke jan zarensa a Kannywood, musamman yadda masu kallon fina-finan Hausa suke son kallon fina-finansa. A tattaunawarsa da Aminiya, daraktan wanda ake yi wa lakabi da Kwankwason Kannywood ko Mai Daraja, ya bayyana yadda ya shiga harkar da yadda ya shigo da sababbin jarumai da kuma kama shi da Hukumar Tace Fina-Finai ta Jihar Kano ta yi a kwanakin baya:

Mene ne takaitaccen tarihika?

Sunana Sunusi Hafiz, wanda aki sani da Oscar. An haife ni a Karamar Hukumar Fagge a Jihar Kano. Na yi makantar firamare da sakandare duk a Fagge, na yi karatun addini bakin gwargwado. Na taso cikin maraici domin ina karami mahaifina ya rasu. Wannan ya sa aka shiga cikin gwagwarmayar rayuwa har daga baya na shigo Masana’antar Kannywood.

Na samu sunan Oscar 442 ne a kwallon kafa. Domin ban taba tunanin ba zan ci abinci a kwallon kafa ba. Amma cikin ikon Allah sai ga ni a Kannywood ina cin abinci. Komai nawa fim ne a yanzu, kuma ina godiya ga Allah.

Yaya aka yi ka tsinci kanka a Masana’antar Kannywood?

Kusan shekara 25 ko sama da haka, na kasance ma’abucin son kallon dirama ta dabe. A unguwar da muke ana irin wannan dirama, hakan ya sa muke zuwa kallo idan mun tashi daga makaranta. Daga nan sai muke ganin duk da cewa muna yara amma akwai kuskure a ciki, daga haka muka fara ba da shawara. Daga nan har muka kai ga karbar shugabancin wajen. Wannan ya sa na ga ya kamata mu ci gaba daga inda muka tsaya domin mu fadada sakon da muke isarwa don duniya ta shaida. Sai muka yi shawarar yin fim, sai ya kasance wadanda muke tare da su ba za su iya daukar nauyi ba, sai na dauki nauyi, kuma na fito a jarumi. Kuma cikin ikon Allah aka samu nasara a wannan fim din. Wannan shi ne yadda aka faro.

Me ya sa ka zabi ka zama darakta?

Na fara fim a matsayin mai shirya fim ne, sai na ga irin kura-kuren da ake yi, wannan ya ba ni sha’awar in fara ba da umarni, kuma na gwada na samu nasara. Domin tunda na fara aikina zuwa yanzu, ban taba samun wani kalubale ba na wani abokin aikina ya ce bai yi masa ba, ko dan kallo ya ce bai yi masa ba. Da a ce na samu wani kalubale cewa bai yi ba, da na ajiye bangaren domin masa’antar tana da fadi.

Wane fim ka fara ba da umarni?

Fim din da na fara shi ne ‘Abin Da Ka Shuka’, kusan shekara 23 ko 24 da suka wuce ke nan.

Mene ne burinka a bangaren ba da umarni?

Burina a bangaren ba da umarni shi ne wata rana in zama darakta a Nollywood ko Bollywood. Wato a kullum ba na kallon kaina a matsayin wanda zai kare rayuwarsa a Kannywood, kullum tunanina shi ne yadda zan ci gaba.

Ana alkanta ka da Tamil Nadu, masu karatu za su sanin mene ne wannan?

Tamil Nadu wata jiha ce a Kudancin Indiya kuma suna da masana’antarsu mai zaman kanta. Abin da ya sa muke lakabi da ita shi ne kasancewar mutane ne masu basira da labarai masu ma’ana, amma saboda an fi sanin bangaren Bollywood na cikin Indiya, sai ba a san da su ba. Kuma akasari ma labarinsu ake dauka a yi amfani da su a Indiya kuma a yi nasara. Wannan ya sa saboda mu din ma da mutanenmu ba su fahimce mu ba, kuma ba cika baki ba, ga shi yanzu mun iya, kuma muna kawo yara wadanda suka kware, muna kuma kawo abubuwan zamani. Ka ji abin da ya sa muke kiran kanmu Tamil Nadu. Yanzu yaran da muka koyar su ne suke jan ragamar Kannywood.

Yaya alakarka da sauran ’yan fim?

Alakata da sauran ’yan fim alaka ce mai kyau musamman masu son ci gaban Kannywood. Idan ka ga muna rigima da wadansu a masana’antar to mutane masu son dunkusar da ita ce amma mutane ba su san su ba. Ba za mu zauna mu zuba ido muna kallo a bata mana masana’anta mu yi shiru ba. Amma a cikin kashi 100, muna da alaka da mai kyau da kashi 85. Ka ga kuwa muna da alaka mai kyau ke nan. Kashi 15 din su ne fitinannun, kuma da sannu za mu sanar da duniya halin da ake ciki a kansu. Abin da suke yi daban, Kannywood daban sannan a rika mana kallon daya muke.

Wane jarumi ka fi son aiki da shi?

Ina son kowane jarumi musamman wanda zai ban lokacinsa. Idan ka ga darakta ba ya son jarumi, shi ne idan ya kasance za ka ba jarumi kudi mai yawa, amma ya zo yana nuna cewa yana taimakonka ne. Ya zo ya rika fada yana cewa a yi sauri a gama da shi, shi wannan fim kwana biyu kawai ya bayar, shi ya gaji da fim din. Ka ga wannan ai ba za ka so shi ba.

Me za ka ce game da rikice-rikicen da ake yi a Kannywood?

Maganar gaskiya dole a yi rikici a Kannywood domin babu inda ba a rikici, musamman mu da Allah Ya hada mu da mutanen banza, azzalumai, amma mutane a waje suna yi musu kallon su ne mutanen kirki. Sannan ga munafunci, mutum ya hada ka fada da wani, sannan ya dawo daga baya ya ce zai shirya ku. Duk mutanen Kannywood sun gane wadannan matsaloli kuma muna nan muna shirye-shiryen magance su. Mun yi magana da manyan malamai a Kano da manyan attajirai da wadansu daga cikin jagororin talakawa. Kuma mun bayyana musu halin da ake ciki a Kannywood na rikice-rikicen kuma su wane ne suke jawo rikicin domin kada a ce babu su. Amma duk rikicin da ka gani a Kannywood daga inda ya fara fitowa daga nan yake fitowa har yanzu, kuma ba zai daina fitowa ba har sai mun yi maganinsa.

A kwanakin baya Hukumar Tace Fina-Fainai ta Jihar Kano ta kama ka, me za ka ce?

Game da kama ni da aka yi, a cikin sharadin belina an hana ni magana da ’yan jarida kuma har yanzu magana na kotu, don haka ba zan ce komai ba.

Amma ana zargin sa hannun wadansu a kama ka da aka yi, me za ka ce?

Abin da wadansu suke zargi, tabbas idan aka bi, za a ga cewa suna da gaskiya. Ba ma zargi ba, tabbataccen abu ne. Amma wani lokacin muna yin shiru ne saboda idan ka fadi wani abu kamar ka rusa kanka ne. Amma dole wata rana mu fito mu cire wannan zargi da ake yi wa wadansu, wadansu kuma mu bar su domin suna aikata abin da ake zargin.

Kana da kira ga ’yan fim?

Kirana ga ’yan fim shi ne mu zauna lafiya mu so junanmu. Babu wata kasa ko al’umma da ta ci gaba ba tare da zaman lafiya ba. Sai mun so junamu don Allah, mu ki mutum don Allah. Wanda ya yi daidai a dafa masa, wanda ya yi ba daidai ba a yake shi, domin gobenmu ta yi kyau. Sannan hukuma kuma ina kira gare su da duk abin da aka kawo musu, su rika yin adalci.

Kana da kira ga masoyanka?

Kirana ga masoya shi ne kada ku bari in rika yin abin da ba daidai ba. Idan na yi ba daidai ba, ku fada min domin ni dan Adam ne kamar kowa. Da zarar kun ga na yi kuskure ku fada min, wannan shi ne soyayya ta gaskiya. Amma idan na yi kuskure ka yi shiru, kamar ba soyayya ba ce.

Kana ganin sinima za ta iya magance matsalar tabarbarewar tattalin arzikin Kannywood?

Eh, amma sai an koya wa mutane. Domin babu wani malami ko attajiri da za ka ga ya tafi kallon fim din Hausa domin kullun abin daya ne. Wadansu mutane ne kawai suka mamaye komai, kullum labarin iri daya kuma jaruman iri daya. Amma idan Allah Ya ba mu dama, za mu canja komai, za mu zo da labarai masu kyau da jarumai da suka fi kamata a ba su dama. Wannan zai sa mutane su koma suna kallon fim, duk girman mutum zai zo ya zauna ya kalli fim kamar yadda ake yi a sauran kasashe.

Idan muna so masana’antar ta ci gaba dole mu tashi mu yaki bara-gurbin cikinmu, amma idan muka bar su, za su karya masana’antar.