✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Musulunci yana koyar da kyawawan halaye ne

Babban Limamin Masallacin Nagazi – Ubete, Okene Jihar Kogi Fassarar Salihu Makera MukaddimaYa bayin Allah! Kyawawan halaye suna daga cikin muhimman abubuwan da Musulunci ya…

Babban Limamin Masallacin Nagazi – Ubete, Okene Jihar Kogi

Fassarar Salihu Makera

Mukaddima
Ya bayin Allah! Kyawawan halaye suna daga cikin muhimman abubuwan da Musulunci ya ba fiffiko, wadanda ta samunsu ne za mu iya samun tsira a gobe kiyama. Kyakkyawar dabi’a babbar alama ce ta koyarwar Alkur’ani da Hadisin Annabi (SAW). Ana gane mutumin kirki ta hanyarta kuma mafiya alherin Musulmi su ne wadanda suke da kyawawan halaye. Muminai masu cikakken imani wadanda Allah Ya fi so da kuma ManzonSa, su ne masu kyawawan halaye.
Musulmin kirki shi ne mutumin da ya samu kyakkyawar tarbiyya daga iyayensa. Don haka ba zai zaga ko ya ci mutuncin shugabansa da manyansa da sauran mutane ba, kuma ba zai saurara wa marasa tarbiyya su yi kokarin zubar masa da mutunci ko su bata masa suna ko su yada karya don bata sunansa ba. Domin ya yi imani cewa hakan rashin tarbiyya ce ke sa mutum ya rika yin haka.
Allah Ya yabi kyakkyawan hali da dabi’un Annabi (SAW) kuma Ya sanya shi ya zamo abin koyi ga dukkan Musulmi. Allah Madaukaki Ya ce: “Kuma lallai, hakika kana a kan halayen kirki manya.” (k:68:4). Masu tafsiri sun ce “Halayen kirki manya” da aka ambata a ayar na nufin Alkur’ani da Annabi da shi kansa addinin Musulunci.
Imam Ibn Kasir ya yi sharhi kan wannan aya da cewa: “Ma’anar wannan aya ita ce, Annabi (SAW) yana koyi da Alkur’ani a umarce-umarce da hane-hanensa, ya zamo shi ne ma’auninsa. Alkur’ani ya zame masa jiki a dabi’u da halayensa ta yadda ya rabu da dabi’arsa ta mutumtaka. Duk abin da Alkur’ani ya yi umarni shi yake yi, abin da ya hana kuma yana guje masa. Tare da haka, Allah Ya dasa masa kyawawan halaye na saukin kai da kyauta da jarumta da yafiya da hakuri da duk wata kyakkyawar mu’amala.” (Tafsirin Alkur’anil Azim, sura ta 68, aya ta 4).  
Babbar manufar aiko Annabi (SAW) ita ce ya dasa kyawawan halaye a tsakanin Musulmi cikin kowane fanni na rayuwarsu. Abu Huraira (RA) ya ruwaito cewa: “Manzon Allah (SAW) ya ce: “Hakika an aiko ni ne, domin in cika kyawawan halaye.” (Musnad na Ahmad, 8729)
A wata ruwayar Annabi (SAW) ya ce: “Iyaka an aiko ni ne domin in cika kyawawan halaye.” (Muwadda, 1614).
A wata ruwayar Annabi (SAW) ya ce: “Hakika Allah Ya aiko ni ne domin in cika kyawawan dabi’u kuma in cika ayyuka na kwarai.” (Mujma’a al-Awsat, 7073).
’Yan uwa maza da mata! Kyakkyawar dabi’a a wurin Allah na nufin ka yi riko da akida mai kyau da yin ayyukan ibada. A wurin mutane kuma, kyakkyawar dabi’a ko hali na nufin ka yi adalci, ka zamo mai tausayi, mai yafiya mai kirki, mai kyauta kuma mai hakuri a wajen mu’amala da su.
Za mu iya ganin hakikanin yadda kyan halin Annabi (SAW) ya kasance lokacin da yake wa’azi a Makka da kuma daukacin rayuwarsa. Sahabbai (RA) sun rika bayar da bayanin yadda kyan halinsa ya kasance babbar hanyar koyarwar Musulunci da suka taba ji a rayuwarsu.
Ibn Abbas (RA) ya ruwaito cewa: “Lokacin da Abu Zarri ya ji Annabi (SAW) ya bayyana a Makka, sai ya ce wa dan uwansa, “Ka hau zuwa wancan gangare ka nemo min labarin wannan mutum da yake  da’awar ana saukar masa da wahayi daga sama. Ka saurari kalamansa sannan ka gaya min. “Sai mutumin ya hau (dabbarsa) har ya isa Makka kuma ya saurari Annabi (SAW), sannan ya koma ga Abu Zarri ya ce: “Na gan shi yana umarni da kyawawan  halaye masu girma kuma maganganunsa ba waka ba ne.” (Muslim, 2474).
Tunda kyakkyawar dabi’a ko kyan hali na da matukar muhimmanci, don haka nuna hali nagari ya zama wajibi a addini. Annabi (SAW) ya umarci Musulmi su rika nuna hali nagari a kowane al’amari, kuma ga dukkan mutane, ba wai sai makusantansu kawai ba.
Abu Zarri (RA) ya ruwaito cewa: “Annabi (SAW) ya ce: “Ka yi mu’amala da mutane da kyakkyawar mu’amala.” (Sunan Tirmizi, 1987).
Hali nagari ba abin so kadai ba ne a addini, a’a kyawawan halaye su ne ruhin addininmu. Su ne batutuwan da Alkur’ani ya yi ta maimata magana a kansu. Ana iya gano kyawawan halaye ta tunanin da Allah Ya sanya a zukatanmu domin mu rika bambance aikin kwarai da zunubi koda ba a aiko da wahayi ba.
An-Nawwas Ibn Sam’an ya ruwaito cewa: “Manzon Allah (SAW) ya ce: “da’a ita ce kyakkyawar hali, zunubi kuma shi ne abin da yake damunka a zuciya amma kake kin mutane su san shi.” (Muslim, 2553). A wata ruwayar kuma Annabi (SAW) ya ce: “Ka tambayi ranka, ka tambayi zuciyarka. da’a ita ce abar da ke gamsar da ranka da zuciyarka, zunubi kuma shi ne abin da yake kaikayi a zuciyarka yake kuntata maka kirjinka, koda mutane sun yi maka hukunci, kuma sun sake yi maka hukunci a kansa.” (Sunan Ad-Darimi, 2533).
Daga wadannan nassoshi da sauransu, fitattun malamai suka fahimci cewa kyakkyawar dabi’a ko hali wani babban ginshiki ne da Musulunci yake bukata kuma shi ne ma addinin.
Imam Ibn Al-kayyim ya ce: “Addini gaba dayansa kyawawan halaye ne, don haka duk wanda ya fi ka kyan hali ya fi ka a addini.” (Madarij as-Salikin, 2/294). Kuma ya sake cewa: “Kyakkyawan hali shi ne addini gaba daya.” (Madarij as-Salikin, 2/363).
Ma’auni na gane Musulmin kirki, shi ne na gano kyakkyawan hali da dabi’arsa musamman a mu’amalarsa da iyalinsa da sauran jama’a. Ana bukatar maza su kyautata wa matansu kyautatawa. Kuma girman Musulmi na bayyana kai-tsaye game da halayyarsa wajen kula da matansa.
Abdullahi Ibn Amir ya ruwaito cewa: “Manzon Allah (SAW) ya ce: “Mafi alherinku shi ne mafi kyawun halinku.” (Buhari,  3366). A wata ruwayar (SAW) ya ce: “Mafiya cikar imani a cikin Musulmi, su ne wadanda suka fi kyawun hali, kuma mafiya alherin cikinku su ne wadanda suka fi kyautata wa matansu.” (Sunan Tirmizi,1162). Kuma a wata ruwayar (SAW) ya ce: “Hakika, cikakkun muminai su ne mafiya kyawun hali da kuma wadanda suka fi kyautata wa iyalansu.” (Sunan Tirmizi, 2612).
Ya bayin Allah! Kyakkyawan hali na daga cikin ayyukan kwarai da za a sanya a mizanin bawa a Ranar Hisabi, har ma ya fi ayyukan ibada na tadawwa’i lada.
Abu Darda’i (RA) ya ruwaito cewa: “Manzon Allah (SAW) ya ce: “Babu abin da ya fi nauyaya mizaninin mumini a Ranar Hisabi kamar kyawawan halayensa. Kuma lallai, Allah  ba Ya son mutum marar kunya mai yawan rantsuwa.” (Sunan Tirmizi, 2002).
A’isha (RA) ta ruwaito cewa: “Manzon Allah (SAW) ya ce: “Lallai Musulmi zai kai matsayin wanda yake yawan azumi da sallolin nafila cikin dare, saboda kyakkyawan halinsa.” (Sunan Abu Dawud, 4798).
Annabi (SAW) ya nuna cewa kyakkyawan hali yana jagorantar mutane zuwa ga shiga Aljanna. A gefe guda kuma mugun hali da ya hada da muguwar magana da zagi ko bata wani da cin mutunci ko zarafin mutane da zina da sauransu zuna jagorantar mutane zuwa shiga wuta.
Abu Huraira (RA) ya ce: “An tambayi Annabi (SAW) cewa: “Me ya fi shigar da mutane cikin Aljanna?” Sai Manzon Allah (SAW) ya ce: “Gaskiya da kyakkyawan hali.” Kuma aka tambaye shi, “Me ya fi shigar da mutane wuta?” Sai Manzon Allah (SAW) ya ce: “Baki da farji.” (Sunan Tirmizi, 2004).
Masu kyawun hali za su kasance a kusa da Annabi (SAW) da sauran mutanen kirki a cikin Aljanna, yayin da wadanda suke aikata miyagun halaye za su kasance nesa da su. Abdullahi Ibn Amru ya ce: “Manzon Allah (SAW) ya ce: “Ko in gaya muku mutumin da na fi so kuma ya fi kusa da ni a Ranar kiyama? Su ne wadanda suke da kyakkyawan hali.” (Musnad Ahmad, 6696). A wata ruwayar (SAW) ya ce: “Hakika mafi soyuwa da kusanci da ni a taron Alkiyama su ne wadanda suka fi ku kyakkyawan hali. Kuma hakika mafiya kyama a wurina daga cikinku kuma mafiya nesa da ni a taron RanarAlkiyama su ne masu alfahari, masu almubazzaranci, masu girman kai.” (Sunan Tirmizi, 2018).
Ya ’yan uwa masu girma! Malamai sun rubuta littattafai da makaloli da dama kan kyawawan halaye, wadanda suke haifar da samuwar tausayawa da adalci da daidaito da hakuri da danne zuciya da saukin kai da tawali’u da kyauta da karimci da jin kai da sauransu ga dan Adam. A takaice kyawawan halaye sun kunshi girmama Allah da girmama dan Adam da dabbobi a matsayinsu na halittar Allah.
Ibn Taimiyya ya takaita bayani kan kyawawan halaye a Musulunci cikin fadinsa: “Musulmi suna karfafa mutane su sulhunta da danginsu da suka yanke dangantaka da su, su bayar da kyauta ko sadaka ga wadanda suka hana su, su yafe wa wadanda suka zalunce su. Kuma suna umartar mutane su kasance masu kyautata wa iyayensu, su kula da zumunta su kyautata wa makwabta, su tausaya wa marayu da matafiya da matalauta, kuma su rika tausaya wa ’yan aikin gida da barori. Suna hana jiji-da-kai da girman kai da zalunci. Suna hana mutane jin sun fi sauran jama’a, koda sun fi su ko a’a. Suna umartar mutane da sanyin hali, suna hana su daga aikata duk abin da zai zubar da mutuncinsu. Duk abin da za su ce ko za su aikata daga wadannan kyawanan halaye da sauran koyarwar ya zamo sun bi Alkur’ani da Sunnah. Hanyarsu ita ce addinin Musulunci wanda Allah Ya aiko Annabi Muhammad (SAW) da shi.” (Al-Akida al-Wasitiyyah, 1/71).
Ya bayin Allah! A matsayinmu na Musulmi, burinmu ya zamo mun rayu yadda Allah Ya ce, ta hanyar ci gaba da neman ilimin addini tare da yin ayyukan ibada, yayin da kuma muke kyautata wa sauran mutane da tabbatar da adalci da gaskiya da rahama da kuma saka mummunan aiki da kyakkyawa.
Ya Allah Ka sanya mu daga cikin wadanda suke samun gafararKa, kuma Ka kare mu daga azabar wuta.
Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai. Tsira da amincin Allah su tabbata ga shugabanmu masoyinmu Annabi Muhammad (SAW) da alayensa da sahabbansa.
Babu taimako face daga Allah Ubangijin halittu, Mabuwayi, Masani.
Imam Murtada Gusau, Babban Limamin Masallacin Juma’a na Nagazi-Ubete da Masallacin Alhaji Abdurrahman Okene, Okene Jihar Kogi.
Za a iya samunsa ta lambar waya: +234 80 3828 9761.