✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Musulunci a tsakanin sakacin mabiyansa da mugun shirin makiya (2)

Fafatawarmu da Yahudawan Isra’ila zai ci gaba matukar duniya ba ta san yanayin gwagwarmayarmu ba, ko kuma da gangan ta ki daukar matakin da ya…

Fafatawarmu da Yahudawan Isra’ila zai ci gaba matukar duniya ba ta san yanayin gwagwarmayarmu ba, ko kuma da gangan ta ki daukar matakin da ya kamata. Ya bayin Allah! Wannan al’amari ya sha bamban da saura. Ya shafi al’amarin Musulunci ne da Musulmi kai-tsaye, amma sai ga shi Isra’ila tana kokarin lullube karya da gaskiya ta wajen nuna matsala ce ta Palasdinawa da Isra’ila

Lokacin da yakin ya tsaya, sai Manzon Allah (SAW) da sahabbansa suka gano gawarsa, suka binne shi da kayan jikinsa, saboda shi shahidi ne, da jinin jikinsa a ranar Kiyama zai rika kanshi kamar na turaren muski. Kuma ba a Sallar janaza ga wanda ya yi mutuwar shahada, saboda shi rayayye ne kamar yadda Allah Ya ce, “Kada ku ce, ga wadanda ake kashewa a cikin tafarkin Allah; “Matattu ne.” A’a rayayyu ne, kuma amma ba ku sansancewa.” Shahada wata gimamawa ce da ake bayar da ita ga masu gaskiya kawai. Ma’aiki (SAW) ya binne Mus’ab a cikin rigarsa, wacce ba za ta iya rufe masa kafa ba idan aka rufe masa fuska da ita saboda gajartarta. Don haka sai Ma’aiki (SAW) ya ce: “Ku rufe kansa da rigarsa, sannan ku rufe kafafunsa da ganye.” Buhari da Muslim suka ruwaito.

Ya ku Musulmi! Mus’ab ya zama shahidi, ya mutu kamar yadda sauran mutane za su mutu, amma abin tambaya Musulmi nawa ne a yau suka san yadda za iya rike tutar Musulunci su kare ta? Ko sun makale ne kan a ci gaba da bi tare da dogaro da manyan azzaluman duniya?

Amurka ba za ta iya kare ku ba, kuma ba za ta iya kubutar da ku daga zaluncin da ake yi muku ba. Ku koma ga Allah, domin babu wani karfi babu dabara face daga Allah! Shi kadai ne zai iya magance komai. Shi ne mafi bayar da kariya kuma mafi taimako.

Huduba ta Biyu

Dukkan godiya ta tabbata ga Allah, wanda Ya kubutar da mu daga miyagun ayyukanmu, kuma Ya albarkace mu da mafificin Manzanni, kuma Ya sanya muka zama mafificiyar al’umma.

Na shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah Mai kare muminai, Yana tare da wadanda ake zalunta kuma Yana ruguza azzalumai. Tsira da amincin Allah su kara tabbata ga shugaban Manzanni, wanda kamar yadda Imran Ibn Husain ya ruwaito ya ce, “Mafificin karni shi ne karnina, sannan wanda ya biyo shi, sannan wanda ya biyo shi. Daga nan wasu mutane za su rika bayar da shaida ba tare da an neme su ba, za su rika daukar alkawarin da ba za su cika ba, maciya amana ne da ba za a amince da su ba…” Buhari da Muslim suka ruwaito. Ya ku muminai! Kafafen yada labarai suna ta ruwaito sabon shirin Isra’ila na sasanta rikicinta da Paladinu tare da kafa kasar Palasdinu. Wannan tsohon shiri ne da ba zai sami nasara ba, manufarsa a rika yaudarar Palasdinawa, amma Allah Ya sani Yahudawa ba da gaske suke ba, game da ba Palasdinawa ’yantacciyyar kasarsu.

Kawo irin wannan tsohon tunani na Isra’ila yana dada jefa al’ummarmu a cikin wahala ne kawai. Gaskiyar magana Yahudawa suna son su karya lagon jajircewarmu ne kawai, tare da ci gaba da mamayar da suke yi mana, ta yadda za a koma da baya daga gwagwarmayar Intifadah da muka faro. Babban hadari ne a goyi bayan kiran kafa kasar Palasdinu bisa tsarin da ke hana Palasdinawa komawa yankunansu, ya yi fatali da damar dawo da yankin Al- Ghour ga Jordan ko Jarusalem ga Palasdinu, kuma ya bukaci Palasdinawa su amince da halaccin kasar Isra’ila, kafin a fara tattauna batun janyewar Isra’ila daga Yammacin Kogin Jordan.

Fafatawarmu da Yahudawan Isra’ila zai ci gaba matukar duniya ba ta san yanayin gwagwarmayarmu ba, ko kuma da gangan ta ki daukar matakin da ya kamata. Ya bayin Allah! Wannan al’amari ya sha bamban da saura. Ya shafi al’amarin Musulunci ne da Musulmi kai-tsaye, amma sai ga shi Isra’ila tana kokarin lullube karya da gaskiya ta wajen nuna matsala ce ta Palasdinawa da Isra’ila.

Isra’ila ta goyi bayan Amurka ta kaddamar da kazantaccen yakinta a kan Musulmi da kungiyoyin Musulunci a sassan duniya. Amurka tana amfani da bama-bamai mafiya muni a kan Musulmin Afghanistan, kuma ta kebe kusan Dala biliyan 70 don yaki da Musulunci. Amurka ta sa kafa ta shure duk wani kuduri na Majalisar Dinkin Duniya da ya shafi taimaka wa Palasdinawa, to ta yaya za a tsammaci Amurka ta taimaka mana, ko ta yi mana adalci?

Birtaniya (kanwa uwar gami wajen kafa haramtacciyar kasar Isra’ila da ta mamaye kasar Palasdinu) kuwa umurtar dakarun Palasdinawa take yi kan su murkushe kungiyoyin Musulunci. Sun manta cewa su ne kan gaba a fagen ta’addanci-ta hanyar yi wa Musulunci da Musulmi ta’addanci. Rasha kuwa kokari take yi ta murkushe kungiyoyin Musulunci da suke cikin kasarta, don haka take kare Isra’ila.

Ya ku Musulmi! Matsin da ke yi wa Palasdinawa su dakatar da Intifada, ya zo daidai da juya baya daga shugabannin Larabawa ga Palasdinawa. Isra’ila da kafafen labarai na Yahudawa a sassan duniya, suna wasa da hankalin mutane kan kai hari ga Iraki da Siriya da Iran, bisa da’awar cewa kasashe ne da suke barazana da tsaron lafiyar Isra’ila.

Don haka daga kan wannan tsarkakakken wuri, daga kan wannan Mumbari mai daraja, nake kira ga dukkan Musulmi da cewa: “Ya ku Musulmi! Ku farka daga gyangyadin da kuke yi! Ku hada kanku! Ku sani kowace kasa daga cikin kasashenku ana iya kai mata farmaki a bayan Afghanistan. Ku hada kanku ta kowane hali ko zamo kasa guda maimakon zama kasashe mabambanta. Makiyanku suna son shafe ku daga bayan kasa, su wulakanta tsarkakan wuraren ibadarku, suna urin a ce, an rasa mai furta La ilaha illallah Muhammadur Rasulullah. Wannan shi ne abin da kawai zan iya fada muku, domin kun dade kuna barci. Kuna wasa da yawa, to amma ku dauki darasi daga kalmomin Ubangijinku.”