✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Musulmi a lokacin kunci da tsanani (1)

Masallacin Juma’a na Al-Mukil Fassarar Salihu Makera Hamdala da taslimi: Bayan haka, ku ji tsoron Allah Madaukaki ku yi maSa da’a, kuma ku tsayar da…

Masallacin Juma’a na Al-Mukil

Fassarar Salihu Makera

Hamdala da taslimi:

Bayan haka, ku ji tsoron Allah Madaukaki ku yi maSa da’a, kuma ku tsayar da addini gare Shi, ku mika maSa wuya, ku mayar da hankalinku gare Shi. Domin babu wurin gudu babu matsera face zuwa gare Shi. Babu mai kubutarwa daga abubuwan ki face yin addu’a a gare Shi. Babu tabbata a kan gaskiya face da tabbatarwarSa. Babu karfi babu dabara ga bayi face naSa. “Ku yi da’a ga Allah kuma ku yi da’a ga Manzon (Allah), idan kuka juya baya abin sani babu wani abu a kan ManzonMu face isarwa mabayyaniya. Allah Wanda babu abin bautawa da gaskiya face Shi, kuma a kan Allah sai muminai su dogara.” (Tagabun:12-13).

Ya ku mutane! A lokacin da bakin ciki ya sauka ga bawa, bai damuwa da abinci da abin sha da barci, har sai ya kawar da shi ko ya gushe masa, zai yi ta neman wanda zai taimaka masa a kansa. Lokacin da mutanen Annabi Lud (AS) suka kewaye shi suna nufin yin ta’addanci ga bakinsa sai ya ce: “Ina ma ina da wani karfi (da zan hana ku), ko kuma in koma ga wani rukuni mai karfi (da za su taimake ni).”  (Hud:80). Annabi (SAW) ya ce “Allah Ya yi rahama ga Lud. Hakika ya koma ga wani rukunin mai karfi.” Muttafakun. Yana nufin rukunin Allah Madaukaki wanda duk ya nemi tsari da Shi ba ya jin kunya. Hakika Lud da sauran Manzanni (AS) sun nemi tsari da Shi, kuma Allah Madaukaki Ya kubutar da su, kuma Ya hallakar da masu karyatawa.

Lallai duniya gidan bala’i ne da kunci ga bayi, gidan jarrabawa kan wadata da tsanani. “Kuma za mu jarraba ku da sharri da alheri a matsayin fitina, kuma gare Mu kuke komawa.” (Anbiya:35). Wannan bala’in daga ciki akwai wanda yake shafar mutum shi kadai kamar talauci da ciwo da damuwa da kunci da makamantansu. Kuma akwai bala’in da ke game jama’a ya shafi gari ko ya watsu ya shafi kasashe ko ya kasance mafi watsuwa ya shafi daukacin duniya.

Bisa lura da masdarinsa, bala’i na iya kasancewa kaddara yanke ta yadda dan Adam bai iya yin komai a kai, koda ya kasance saboda zunubansu ne, kamar girgizar kasa da ambaliyar ruwa da annoba da makamantansu. Akwai kuma abin da ke aukuwa sakamakon zaluncin dan Adam ga dan uwansa, kamar jawo yunwa da talauci da hasara da boye kaya da kai hare-haren ta’addanci da sauransu.

Wadannan masifu da bala’o’i suna karuwa kuma suna tagayyara muminai a tsawon zamunna, wannan saboda ka’idar nan ce da ke cewa “Babu wata shekara face mai biye mata ta fi ta sharri, har sai kun koma ga Ubangijinku.” Kamar yadda Annabi (SAW) ya ba da labarin haka.

Idan aka lura da bala’o’in wannan lokaci, aka lura da masifu a jumlatance, aka bibiye su, za a ga bala’o’i ne da suke shafar mutane da yawa, ja’ircinsu na kawo hallaka mai yawa da talauci da wargajewar al’amura, ’yan kasuwa su rasa dukiyarsu baki daya ko mafi yawanta, tsoro mai tsanani ya lizimce su, suna haifar da masifu masu yawa da dayansu ke buwayar masu karfi, to, ina ga a ce dukansu sun hadu?

A lokacin da wadannan masifu suka rika maimaituwa a garuruwa da kasashe, sai wadanda ba su isa gare su ba, su rika tsoron haduwa da su, musamman idan masana da kwararru suka ba da labarin cewa bala’i da annoba da alamun ambaliya ko girgizar kasa suna karuwa, inda masana rayuwa da harkokin siyasa da masu hangen nesa za su hadu cewa za a fuskanci matsaloli a fagen tattalin arziki da siyasa da zamantakewar kasa a nan gaba.

Don haka babu abin zargi a kan mutane idan suka ji tsoro kan rayuwarsu da ’ya’yansu da gidajensu da dukiyarsu, suka rika tunanin abin da zai faru da su a gaba. Domin jin dadin rayuwa yana tare da zaman lafiya ne a koyaushe, kamar yadda tabarbarewar rayuwa ke tare da susucewar zaman lafiya da azabar rayuwa da tashin hankali.

Sai dai duk da haka, muminai suna da wurin fakewa da suke komawa gare Shi. Idan suka nemi tsari da Shi, Shi Mai tsarewa ne, idan suka lizimce Shi, zai lizimce su. Shi ne ke ba da kariya idan rayukan da suka fada cikin matsala suka yi imani da Shi. Zukatansu suka natsu da Shi, koda sauran mutane sun kauce maSa. Duk lokacin da zuciyar bawa ta kullu a kan imani da yakini, ta cika da tawakkali ga Allah, ba ta ta’allaka da kowane sababi ko yaya yake ba, ba ta yi kwadayin komai daga wanin Allah ba, kuma ba ta tsoron waninSa. Ya zamo zuciya tana sane cewa duk abin da ya auku bisa kaddararSa ce Madaukaki, kuma dukan komai yana karkashin tankwarawarSa da karfinSa ne Mai girman Daraja. Suna masu mika wuya ga hukuncinSa da umarninSa. A lokacin ne rayuka za su samu hutu su iya magance bala’insu, kirjinsu ya fadada, zukatansu su samu natsuwa, ba su tsoron kowa, ba su tsoron aukuwar komai. Hakika Allah Madaukaki Ya ce: “An kankare musu kananan zunubansu, kuma an kyautata rayuwarsu.” (Muhammad:2).

Duk wanda aka kyautata masa, sai tunaninsa ya daidaitu shu’urinsa ya daidaita, zuciyarsa da lamirinsa su natsu, ransa ya samu aminci da zaman lafiya.

Ibnu Kayyim (Rahimahullah) ya ce: “Tawakkali ga Allah hakikanin tawakkali zai iya kawar da dutse daga muhallinsa, idan aka umarce shi ya kawar da shi.”

Tawakkali ga Allah ne ya sa Annabawa (AS) suka samu nasara a kan duk masifun da suka same su da wahalhalun da suka mamaye su. Sun sanya tawakkali guzurinsu a lokacin tsanani, sun rike shi makamin yakar ma’abuta kaidi. Mutanen Annabi Ibrahim (AS) sun taru sun hura wuta ganga-ganga domin kone shi, amma sai aka tserar da shi daga gare ta saboda tawakkalinsa ga Allah!

Sannan kungiyoyi sun hadu a kan Annabinmu Muhammad (SAW), sai Allah Ya kunyata su, saboda tawakkalinsa ga Allah. Ibn Abbas (RA) ya ce: “Hasbunallhu wan ni’imal wakil.” Annabi Ibrahim ya fade ta lokacin da aka jefa shi a wuta, kuma Annabi Muhammad (SAW) ya fade ta lokacin da suka ce: “Lallai mutane sun hadu (domin yakarku) domin haka ku ji tsoronsu, sai (hakan) ya kara musu imani, kuma suka ce: “Hasbunallahu wan ni’imal wakil.” (Al- Imran: 173). Buhari da Muslim suka ruwaito.

Kuma a lokacin da aka kori Annabi Musa (AS) da muminan da ke tare da shi, aka kewaye su suka ji tsoron hallaka, ga Fir’auna da rundunarsa a bayansu, ga teku a gabansu, sai tawakkalin Annabi Musa (AS) ga Ubangijinsa ya zamo sauki da sababbin kwaranye musu bakin cikinsu da ceto rayukansu. “A lokacin da jama’ar biyu suka ga juna, sai sahabban Musa suka ce, “Lallai mu ababen riskewa ne.” Sai ya ce: “Ba haka ba ne! Lallai ni, ina tare da Ubangijina kuma da sannu Zai shiryar da ni. Sai Muka yi wahayi zuwa ga Musa cewa ka bugi tekun da sandarka, sai (tekun) ya dare, kowane bangare ya zamo kamar wani dutse mai girma.” (Shu’ara:61-63).

Haka Annabi Yakubu (AS) ya nuna tawakkali lokacin da ya ji tsoron shaidanun mutane da aljanu a kan ’ya’yansa, sai ya yi musu wasiyya sannnan ya ce: “Ba na iya wadatar muku komai daga Allah, hukunci dukansa na Allah ne, a gare Shi nake dogara, kuma masu tawakkali su dogara a gare Shi.” (Yusuf:67).

Shi kuwa Annabinmu Muhammad (SAW) ya nuna hakikanin tawakkali da mafi daukakar tawakkali, kuma ya nuna amincewa da Ubangijinsa a mafi wahalar wuraren zamansa, imaninsa bai raurawa ba, yakininsa bai girgiza ba. Tawakkali ga Allah shi ne mafi girman makaminsa. Mushirikai sun tsaya a bakin kogo suna nemansa, har Abubakar (RA) ya ji tsoro kada su ga Annabi (SAW), sai ya ce: “Idan dai dayansu ya duba kasar kafafunsa zai gan mu.” Sai Annabi (SAW) ya ce: “Mene ne tsammaninka da mutum biyu da Allah ne na ukunsu ya Abubakar?” Muttafakun. Wannan ya nuna cikakken yakini da Allah Madaukaki da wadataccen tawakkali da natsuwa da watsi da kowane dalili daga cikin dalilai face na Allah Madaukaki.