✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Musulman Ukraine sun yi Sallar neman galaba a kan Rasha

Akwai dai Musulmai a sassan Gabashin Ukraine

Musulmai ’yan asalin kasar Ukraine sun gudanar da salloli na musamman don neman galaba a yakin da kasarsu ke gwabzawa da Rasha da kuma neman ganin karshen yakin.

Mufti Said Ismahilov, wani jagoran Musulmai a kasar, mai kimanin shekara 43, wanda yake tare da sojojin kasar a filin daga ne ya jagoranci Sallar ta musamman.

Tun lokacin da aka kaddamar da yaki a kan kasarsa ne ya yanke shawarar jingine harkokin addini don shiga fagen daga a fafata da shi gadan-gadan.

A karshen shekarar da ta gabata, lokacin da alamu suka tabbatar da cewa za a kaddamar da hare-hare a kan kasarsa, malamin ya fara karbar horo daga wata bataliyar sojojin Ukraine.

Amma kafin nan, ya shafe akalla shekara 13 a matsayin mai ba da fatawa a kasar.

An dai haife shi ne a birnin Donetst na Gabashin ukraine, daga bisani kuma ya koma wani gari mai suna Bucha da ke kusa da birnin Kyiv, amma daga baya sai ya tsinci kansa a tsakiyar hare-haren Rasha kace-kace.

“A wannan lokacin sai na yanke shawarar cewa babu inda zan je, zan tsaya a fafata da ni,” kamar yadda ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AP a birnin Kostiantynivka.

Ya ce, “Idan kana da jajircewa za ka iya yaki. Hatta Ma’aiki (S.A.W) da kansa jarumi ne. Saboda haka zan yi koyi da shi, zan tsaya in yi wa kasata yaki,” inji shi.

Akwai Musulmai da yawa dai a yankin Crimea, wanda kasar Rasha ta mamaye a shekara ta 2014, kuma adadinsu ya kai kimanin kaso 12 cikin 100 na mutanen garin.

Bugu da kari, akwai wasu Musulman da dama a yankin Gabashin Ukraine, sakamakon harkokin tattalin arziki da suka sa Musulmai da dama suka yi kaura zuwa yankin Donbas don yin aikace-aikace a wuraren hakar ma’adinai da masana’antu.