Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayyana marigayi Sheikh Ahmed Lemu a matsayin “daya daga cikin muryoyin manyan malamai masu sassaucin ra’ayin addinin Islama, wadanda masu amfani da hikima wajen yada ilimi, wanda hakan ya kara nuna hakikanin hasken da ke cikin addinin.”
Buhari sakon ta’aziyyar fitaccen mmalamin ya ce, “Najeriya da ma Afrika baki daya, sun yi babban rashi na daya daga cikin manyan masana na duk zamunna.”
- Tarihi da rayuwar Sheikh Ahmed Lemu (1929-2020)
- Buhari ya nada Farfesa Duna sabon Daraktan NBRRI
- Sheikh Ahmed Lemu ya riga mu gidan gaskiya
Shugaban Kasar ya ce marigayi Sheikh Ahmed Lemu, “fitaccen malami ne, masanin shari’a, kuma babban marubuci mai baiwar tarin ilimi tamkar wata babbar ma’adana ta tarihi.”
A cewar Shugaban Kasar ta bakin kakakinsa Garba Shehu, “gudunmuwar da marigayi Sheikh Lemu ya bayar ga ilimin addinin Islama da kuma jajircewa wajen tattaunawa da muhawara a tsakanin addinai don fahimtar juna ba za ta misaltu ba”.
Ya ci gaba da kwarara wa mashahurin malamin yabo, inda ya ce mutum ne mai tawali’u wanda ya sadaukar da rayuwarsa tare da bayar da fifiko wajen neman ilimi fiye da komai a duniya.
Shugaba Buhari ya yi addu’ar “Allah Ya karbi ayyukan Sheikh Lemu na alheri musamman gudunmuwar da bayar ga addinin Islama da kuma yadda ya kasance ja-gaba wajen gudanar da zaman tattaunawa da kulla muhawara a tsakanin mabiya addinai a Najeriya da zummar fahimtar juna.
“Allah Madaukakin Sarki Ya jikan sa da Rahama kuma Ya sa Aljanna ce makomarsa. Allah kuma Ya bai wa iyalansa hakurin wannan rashin.”
Aminiya ta ruwaito cewa a safiyar ranar Alhamis, 24 ga watan Disamban 2020, Allah Ya yi wa fitaccen malamin rasuwa bayan ya shafe shekaru 91 a ban kasa.