Mazauna Dakar, babban birnin Senegal sun fito kan tituna a cikin dare cike da murna suna shagulgula bayan tawagar ’yan wasan kasar ta kafa tarihi wajen lashe Gasar Cin Kofin Nahiyar Afirka (AFCON) a karon farko.
Gwamnatin Senegal ta kuma ayyana ranar Litinin a matsayin ranar hutu, bayan tawagar ’yan wasanta sun doke Masar a wasan karshe na gasar a ranar Lahadi da dare.
- AFCON2021: A karon farko, Senegal ta daga Kofin Afirka
- Kungiyar Tarayyar Afirka ta zabi sabon shugaba
Dubban ’yan kasar da ke gida ne suka fito sanye da rigunan tawagar ’yan wasan suna kade-kade da raye-raye a kan tituna, inda suka yi dandazo da babban dandalin nan na Independence Square da ke birnin Dakar.
A sakonsa na bayyana ranar Litinin a matsayin rana hutu, Shugaban Kasar Senegal, Macky Sall, ya ce, “Gwarazan Afirka, lallai kun yi wasa iya wasa mai kayatarwa, kuma hakika kun sanya kasarmu farin cikin, muna alfahari da ku. Muna taya ku murna, jarumanmu.”
Shugaba Sall wanda ya shirya kai ziyarar aiki zuwa kasar Komoros, bayan ya ziyarci kasashen Masar da Habasha, ya dage ziyarar tasa zuwa Komoros domin zuwa gida ya tarbi Zakarun Afikra, da misalin karfe 1 na ranar Litinin a birnin na Dakar.
Murnar ta karade birnin Dakar da sauran sassan kasar ne bayan babban dan wasan kasar, Sadio Mane, da ke taka leda a kungiyar Liverpool a Birtaniya, ya zura kwallon da ya ba wa Senegal nasarar cin Masar 4-2 a bugun fenariti, bayan an tashi wasan babu ci, bayan karin lokaci.
Mane wanda abokinsa kuma dan wasan Liverpool, Mohamed Salah na kasar Masar, shi ne ya zura kwallon da ya kai Senegal ga tudun-mun-tsira; wajen doke tawar su Salah da kuma daga kofin.
Zura kwallon da Mane ya yi ke da wuya, duk inda aka bi a birnin Dakar, jama’a ne ke murna suna sanya hon din motoci, da bushe-bushe da kade-kade, ganin cewa kasar ta kafa tarihi, a karon farko ta lashe kofin, bayan wasa mai zafi tsakaninsu da kasar Masar wadda sau bakwai tana lashe gasar.
Murnar samun nasarar ta karade ko’ina a birnin Dakar, inda dandazon mutanen da suka taru da dandalin Independence Square su yi ta bin manyan tituna cikin murna suna rungumar juna tare da daga tutar kasar, wasu kuma sun rataya ta a jikin gine-gine da motoci da tituna.
“Ina cike da murna, wannan ce babbar ranar farin ciki a rayuwata,” inji Modou Ba mai shekara 25 da ke sana’ar wankin mota.
Nourou Diop mai shekara 27 wanda akanta ne, ya ce, “Da ma mun dade muna jira. Yanzu kuma kofin ya zo hannunmu. Da ma muna bukatar cin kofin.”
Khadim Lo mai shehaka 21, wanda kuma dalibi ne ya ce, “Ina alfahari da ’yan wasanmu. Wannan na musamman ne.”
Tashin hankali: Mane ya barar da bugun fenariti
Kafin busa usur din karshe a wasan, an ga fuskokin wasu mutanen Senegal cike da hawaye a yayin da suke kallon bugun fenariti a wasan karshen. Wasunsu ma ba sa iya kallon talabijin saboda zullumi.
Tun a lokacin wasan kafin cikar lokacin farko, ’yan Senegal suka shiga tashin hankali, ganin cewa Mane ya barar da bugun fenariti da ya samu, wanda golan Masar, Mohamed Abou Gabal, ya buge.
A lokacin da aka zo bugun fenaritin karshe bayan an tashi babu ci, an ji wani direba mai shekara 24, Pape Mbaye, yana fada cikin bacin rai cewa, “Idan Mane ya kuskura ya barar da wannan damar! Bai kamata a wasan karshe babban dan wasa ya barar da damar da ya samu ba. Ba za mu lamunta ba.”
’Yan kasar sun fara samun kwarin gwiwa ne bayan ganin ’yan wasan Masar sun barar da biyu daga cikin bugun fenaritin da suka samu.
A karshe, Mane na zura kwallo a bugun karshe na fenaritin da ya samu, ko’ina ya cika da murna, ganin cewa Senegal ta kafa tarihi.