Fadar Shugaban Kasa ta ce tana bayan Ministan Sadarwar, Isa Ali Pantami dari-bisa-dari, kan bayanin da ya yi game da matsayinsa a baya kan kungiyoyin Al-Ka’ida da Taliban.
A raddinta ga masu neman a sallami Pantami daga matsayinsa, Gwamnatin Buhari ta ce ta gamsu da bayanin da ya yi cewa, ya yi kalaman ne a lokacin da yake matashi, kuma ya dade da yin watsi da matsayi.
- Fursunoni sun ta da bore a babban gidan yarin Kano
- Yadda harin ’yan bindiga ya tilasta rufe sansanin sojoji a Neja
Sanarwar da kakakin Shugaban Kasa, Garba Shehu, ya fitar ta ce, “Abin takaici ne salon da aka bullo da shi na neman dora wa shugabannin siyasa, addini da ’yan gwagwarmaya laifin kalaman da suka yi a baya, alhali yanzu sun sauya matsaya.
“Manufar ita ce neman a muzanta shugabannin ta hanyar fakewa da kalamansu na baya.”
Fadar Shugaban Kasar ta ce, “Salon da yanzu masu karajin neman a sauke Ministan Sadarwa, Dokta Isa Ali Pantami, daga mukaminsa suka dauka ke nan.
“Ba su lura da cewa an shekara 20 da yin maganar da suke neman fake da ita ba, tun da su manufarsu ita ce kawai a sauke shi, sannan ba su da wata hujja face wannan.
“Bukatarsu kawai ita ce a dakatar da shi daga daukar mataka da kuma bullo da tsare-tsaren da za su kara inganta rayuwar jama’ar Najeriya.
“Ministan ya ma riga ya ba da hakuri game da kalaman da ya yi a farkon shekarun 2000.
“Matsayar tasa ta baya ba karbabbiya ba ce, kuma da zai koma kanta a yanzu da ba za a lamunta ba, amma ya fada a bainar jama’a cewa mahangar tasa ta baya kuskure ce, sannan ya nemi afuwa.
“Shekarunsa ashirin da wani abu ne kacal lokacin da ya yi wadancan kalamai da aka magana, amma badi zai shekara 50.
“Yadda lokaci ke tafiya, haka ma mutane da fahimtarsu game da al’amura suke sauyawa, saboda karin fahimtar rayuwa da suke samu.
“’Yan Najeriya masu zurfin tunani sun san cewa an kirkiro da wannan rudanin ne kawai domin kawo masa tarnaki a halin yanzu.
“Gwamnati na bayan Pantami da daukacin ’yan Najeriya wajen ganin an yin musu adalci, sun kuma samu sauki da kuma tsaro a bangaren sadarwar zamani,” inji sanarwar ta Garba Shehu.