Firaministan Birtaniya, Keir Starmer ya buƙaci Donald Trump kada ya ɗauki matakin soji kan Iran, yana mai kiran da a biyo wa lamarin ta hanyar lalama.
Mista Starmer ya ce akwai “mummunan hatsarin bazuwar” yaƙin, inda ya yi kira ga duka ɓangarorin sun rungumi sulhu.
- Ba zai yiwu mu bar Khamenei a raye ba — Isra’ila
- Hisbah ta lalata katan 243 na barasa da wasu kayan maye a Yobe
Ya ƙara da cewa a baya an samu “jerin tattauna masu yawa da Amurka, kuma ina ganin wannan ita ce hanyar warware matsalar.”
Kalaman nasa na zuwa ne yayin da sakataren harkokin wajensa, David Lammy ke shirin ganawa da takwaransa na Amurka, Marco Rubio kan yadda za a taƙaita bazuwar yaƙin.
Da maraicen yau Alhamis ne kuma Mista Lammy da Mista Rubio suka gana domin tattauna halin da ake ciki a yankin Gabas ta Tsakiya.
Su ma shugabannin China da na Rasha sun yi Alla-wadai da hare-haren Isra’ila kan Iran tare da kiran a tsagaita wuta.
Shugaba Xi Jinping da Vladimir Putin sun tattauna ta waya inda suka nuna goyon-bayan amfani da hanyoyin diflomasiya wajen shawo kan rikicin.
Ministan Harkokin Wajen Iran, Abbas Aragchi zai tattauna da takwarorinsa na Faransa da Jamus da Birtaniya a Geneva a gobe Juma’a.