Kungiyar Dattawan Arewacin Najeriya sun bayyana nadamarsu kan zaɓen Shugaban Ƙasa mai ci a yanzu, Bola Ahmed Tinubu.
Tinubu ya yi takara da tsohon mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar dan asalin Jihar Adamawa da ke Arewa maso Gabashin Najeriya.
Atiku Abubakar ya zo na biyu a yawan kuri’un da aka kada, yayin da Peter Obi ɗan Jihar Anambra na jam’iyyar Leba ya zo na uku.
Bayanan Kungiyar Dattawan Arewacin kasar na nuna cewa ba su bai wa ɗan yankin su goyon baya ba a zaɓen da ya gudana a shekarar 2023.
A ganinsu dai yin hakan neman haɗe kan Najeriya ne wuri guda amma dai da alama kwalliya ba ta biya kuɗin sabulu ba.
- Abubuwan da ya kamata Musulmi ya yi a ranar Karamar Sallah
- DAGA LARABA: Yadda ‘Yan Arewa Za Su Samu Kuɗi A Soshiyal Midiya
Dattawan Arewan sun fara zargin Tinubu da har yanzu bai cika shekara guda a kan karagar da zai mulka tsawon shekaru huɗu ba da fara nuna musu cewa kowa na da gidansu.
Kakakin Kungiyar, Abdul-Azeez Suleiman a wata tattaunawa da jaridar Guardian ya bayyana cewa nan gaba za su duba ɗan takarar da zai kwatanta mulki ba tare da bangaranci ba.
Da aka tambayeshi kan yadda suke kallon zagayen shan ruwan azumi da Peter Obi ya riƙa yi a Ramadanan da ya ganata, Abdulaziz ya ce yankin zai ba da fifiko ga wanda ake ganin ya fi kowa ra’ayin Najeriya kasa ɗaya uwa ɗaya kuma uba ɗaya, wanda bai da yawan cece-kuce, kuma wanda ya fi dacewa da muradun ɗaukacin yankunan ƙasar nan.
“Arewa ta yi kuskure wurin zaɓen Bola Tinubu a matsayin shugaban kasa a 2023, kuma da wuya a sake maimaita irin wannan kuskuren nan gaba.
“Mun koyi darasi daga kuskuren da muka yi a baya kuma za mu yi ƙoƙarin zaɓo ɗan takarar da zai iya haɗa kan ƙasar nan tare da gudanar da mulki domin amfanin ‘yan Najeriya baki ɗaya.
“Nan gaba, Arewa za ta yi taka-tsan-tsan wajen zaɓen Shugaban Ƙasa.
“Kuskuren goyon bayan Tinubu a 2023 ya koya mana mahimmancin haɗin kai da fahimtar juna wurin zabar ɗan takarar kujera mafi girma a kasar.”
Tinubu na shan caccaka daga wurin ‘yan Najeriya, musamman akan wasu tsare-tsarensa da ake ganin babu tausayin al’ummar kasar a zuciyarsa.
Ko a farkon makon nan, babban abokin hamayyar Tinubu a zaben 2023 Atiku Abubakar ya ce, babu tausayin jama’a a tsare-tsaren gwamnatin Tinubu.
Sai dai kullum gwamnatin na faɗa wa ’yan Najeriya cewa daɗi na nan tafe, an gama shan wahala.
Duk da yadda ake caccakar muradun gwamnatin, babu alamar akwai wani abu da take niyyar sauyawa dangane bala’in tsadar rayuwa da mummunan talaucin da ’yan ƙasar ke kokawa.