Gwamnnatin Tarayya ta ce matsaloli masu tarin yawa ne suka haddasa karancin wutar lantarki da ake fama da shi a fadin Najeriya.
Ministan Lantarki, Abubakar Aliyu, ne ya sanar da hakan, inda ya ce gwamnati na iya kokarinta domin shawo kan lamarin.
- Duk wanda ya sa N5m a banki a sanar da EFCC —Majalisa
- Matar tsohon Gwamnan Anambra ta tsinka wa matar Ojukwu mari a wajen rantsuwa
Ministan ya tattauna da manema labarai ne bayan kammala taron Majalisar Tattalin Arzikin ta Kasa, wanda Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo ya jagoranta.
Ya ce ruftawar wasu turakun wutar lantarki ne ta haddasa karancin wutar da ake fama da shi a yanzu.
Aliyu, ya ce sauran matsalolin su ne fasa bututun mai da kuma takaddama tsakanin kamfanonin samar da iskar gas da kamfanonin raba wutar lantarki.
Yanzu haka dai matsalar karancin wutar lantarki da kuma rashin mai sun ta’azzara a kusan kowane fanni na rayuwa a Najeriya.
Tasirin matsalolin biyu a kan al’amuran yau da kullum ya sa tuni farashin abubuwa suka yi tashin gwauron-zabo.