✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Muna kokari domin kare mutuncin matasanmu a Kalaba’

Shugaban kwamitin tsaro hadin kai da tabbatar da zama lafiya a Kuros Riba (PSU&P) Alhaji Ya’u Isma’il Girei ya bayar da tabbacin cewa kwamitinsa zai…

Shugaban kwamitin tsaro hadin kai da tabbatar da zama lafiya a Kuros Riba (PSU&P) Alhaji Ya’u Isma’il Girei ya bayar da tabbacin cewa kwamitinsa zai zage damtse, domin ganin matasan Kuros Riba, musamman ’ya’yan ’yan Arewa mazauna jihar, ba su shiga harkoki da za su rika zubar da mutuncinsu da na iyayensu a daukacin fadin jihar ba.

Alhaji Isma’il Gorei ya bayyana haka ne a jawabin marhaba da ya yi  lokacin da wakilan kwamishinan ma’aikatar matasa da wasanni ta jihar karkashin jagorancin babban darakta a ma’aikatar mmista Emmanuel B.Ekpenyong da mataimakiyarsa uwargida Immaculata E. Ekpenyong suka kai wa kwamitin ziyara a ofishin kwamitin da ke layin Bagobiri a Unguwar Hausawa da ke Kalaba fadar gwamnatin jihar. 

A cewar Shugaban PSU&P: “Mun kafa wannan kwamiti ne domin tarbiyantar da ’ya’yanmu da nufin hana su shiga nau’o’in tsageranci da kungiyanci da makamantan duk wani aiki da zai haddasa husuma, kuma domin  mu hada hannu da gwamnatin jiha da ta tarayya wajen bayar da gudunmawa kan harkar  tsaro, saboda larura ce ba ta gwamnatin jiha ko tarayya ba, ya dace kowa ya taimaka domin magance kalubalen tabarbarewar tsaro da galibi ya zama ruwan dare a duniya.”

Kuma ya bayyana gamsuwarsa matuka gaya yadda ya lura matasa da suke zuwa daga jihohin Arewa ci-rani suka rungumi sana’a. 

 “ Ina matukar farin ciki, musamman ma idan naga ’yan uwanmu ’ya’yanmu matasa da suke zuwa cin rani suna neman arziki ba su shiga harkokin kungiyoyi da shaye-shaye. Domin za mu ci gaba da daukar mataki na ganin mun dakile duk wata harka ta shaye-shaye da masu zuwa suna bata mana unguwa.”

Daga nan ya gargadi matasa da su guji sayen kayan sata da cinikin kayan maye. Domin a cewarsa duk wani wanda aka kama zai dandana kudarsa. Idan an samu mutum da laifi babu ruwan kwamitinsa da shi .

A jawabinsa, shugaban ya karkare da yi  wa duk masu neman hadasa husuma da sunan raba kasa cewa, kowa ya yi hakuri tunda Allah ya hada mu kasa daya muzauna tare fitina ba ta da wani amfani kowa ya yi kokarin zama mutumin kirki shi ya fi.

Da yake mayar da jawabi jagoran tawagar Mista Emmanuel Effiong a madadin kwamishinan cewa ya yi “a gaskiya mun gamsu da yadda muka zo muka ga ashe hadda shugabann addini da sarakuna jagoran wannan kwamiti munga  ashe akwai liman da sarki a ciki ai dama tunda sakataren wannan kwamiti Alhaji Sha’aban Abdullahi ya zo neman izinin gwamnati ta yi wa wannan kwamiti rajista muka ce babu wata damuwa. Domin rajistar da za ta kai shekara biyu kafin  a  sabuntata, ganin wadannan manyan mutane masu kima da mutunci da muka gani mun san babu wata tababa.”

“Mun ji dadin yadda kuka shigo domin taya mu bayarda gudunmawa wajen harkar tsaro ai mu dama Jihar Kuros Riba jiha ce ta zaman lafiya, kuma ba za mu taba bari wani ya zo daga wata jiha ko yanki ba ya  cusa mana wata akida  ta daban. Sannan Hausawa kuna da tarihin zama Kuros Riba mai kyau, domin ba a taba samunku a wani ya mutsi ba. Mun gode da kuka shigo wajen taya mu tsaro da zaman lafiya,” inji shi

Ita kuwa uwargida Immaculata Ekpenyong, wadda take kula da horar da matasa a ma’aikatar   da ta mike bayan ta yi wa al’ummar Arewar da shugabannin kwamitin godiya nuna matukar farin ciki ta yi. “Nan gaba gwamnati a shirye take idan za ta yi wa matasan jihar wata bita ko horo na koyar da sana’o’i ma’aikatar su za mu rubuto wa wannan kwamiti ya ba mu matasa da za mu hada su da namu a horar da su ko a koya musu sana’a,” inji ta. Immaculata, ta shawarci kwamitin da ya  shigar da ’yan asalin jihar da ke zaune cakude da ’yan Arewa a unguwar tasu, kuma da a guji daukar doka a hannu da zarar wata matsala ta auku a sanar da ofishinsu .

Alhaji Sani Baba Gombe Sarkin Nasarawa/Bacoco gari na ’yan Arewa tsantsa da ke karamar Hukumar Birnin Kalaba ya tambayi kwamishinar cewa “mu da aka haife mu a Kuros Riba, mu ma  muka haifa ko me ya sa ba a ba mu  shaidar zama  dan kasa da kuma rika daukar mu aikin gwamnati a mataki na jiha tunda nan muka yi karatu akwai ma yaranmu da suka gama manyan makarantu. dan uwana a gaskiya mu a nan Kuros Riba ba za mu iya daukar muku alkawari ba na  daukar aiki a matakin  gwamnatin jiha, nasan ana tafiya da ’yan Arewa a gwamantin jiha, ana nada muku shugaban hukumar alhazai da kuma ba ku damar nada sarakunanku, kuma a wannan gwamnati ai an nada muku mai bai wa gwamna shawara kan baki da ba ’yan asalin jiha ba na  musamman. Shawarar da zan ba ku a nan ita ce ku rika nema musu ta fuskar tarayya idan an kawo wani babban ma’aikaci na tarayya ku rika mika musu bukatunku za su taimaka. Game da shaidar zama dan asalin jihar kuwa cewa ta yi “A gaskiya wannan matsala ruwan dare ce a Najeriya, akwai dan uwana mazaunin Kano ne can ma ya hayayyafa idan wani abu ya taso na karatun ’ya’yansa shi ma gida Kuros Riba yake dawowa yana yi musu ba zan yi karya ba domin a soni,” inji ta.