✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Muna kira ga sauran ’yan Boko Haram su mika wuya — Rundunar Sojin Najeriya

Babu wanda yake so ya ga mutane na mutuwa.

Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya, ta yi kira ga ragowar mayakan Boko Haram da su rungumar zaman lafiya ta hanyar mika wuya.

Sashen Hausa na BBC ya ruwaito cewa, rundunar ta yi wannan kira ne yayin wani baki da ta shirya wa ’yan jarida ranar Lahadi a Maiduguri, babban birnin Jihar Borno.

Babban Kwamandan runduna ta 7 ta sojojin Najeriya, Birgediya-Janar A.A Eyitayo wanda ya yi kiran, ya ce sun fatattaki mayakan a farmakin da sojoji suka kai wanda ya jefa ragowar mayakan da suka tsira cikin rudani.

Janar Eyitayo wanda kuma shi ne Kwamandan daya daga cikin rundunar Operation Hadin Kai, ya yi kira ga sauran mayakan da su rungumi zaman lafiya su mika kansu.

A cewarsa, “Mu kan mu ba mu son zubar da jini, don babu wanda yake so ya ga mutane na mutuwa.”

Ya ce hakan zai ba su damar cin moriyar shirin karbar yi wa tubabbun ’yan Boko Haram afuwa da horar da su a kan sana’o’i gami da gyara musu tunani da halayyarsu su koma rayuwa kamar irin ta kowa.