Nomiis Gee fitaccen lakabi ne a harkar wake-wake, musamman irin na zamani da ake kira hip-hop, a Kano da ma Arewacin Najeriya.
Mai wannan lakabi dai shi ne Aminu Abba Umar, wanda yake kuma gabatar da shirye-shirye a kan salon wakokin na hip hop a gidan talabiji na Arewa24.
A wannan tattaunawa da Aminiya ya musanta zargin da ake yi cewa daya daga cikin shirye-shiryen, “Zafafa Goma”, yana bata tarbiyyar matasa, yana cewa dimbin jama’a suna shiryuwa ta hanyar shirin.
Ko za ka fada mana kadan daga cikin tarihin rayuwarka?
An haife ni a Kano, na yi karatuna na firamare har zuwa jami’a a Kano; na yi hidimar kasa a Jihar Binuwai.
Bayan na dawo gida sai na kama harkar waka gadan-gadan wadda kuma har yau ita nake yi a matsayin sana’a.
Yaushe kuma me ya ba ka sha’awa ka fara waka?
Zan iya cewa ni tashi na yi ina son waka, saboda kasancewar mahaifina dan jarida ne.
Hakan ya sa na tashi da harkar nishadantarwa domin tashi na yi na ji ana jin waka a gidanmu.
To tun ina sakandire na fara yin waka. Lokacin da na shiga jami’a abin ya ci gaba sosai.
Lokacin ina Jami’ar Bayero sai na yi wata waka da ake kira “BUK Town” wacce na wake Jami’ar Bayero a ciki.
To tun daga wannan waka ne hanya ta bude min, ya zamanto an fara sani na.
Daga nan na samu kwarin gwiwa na ci gaba da waka.
Bayan na gama jami’a sai na zauna na yi tunani sosai na fuskanci harkar hip hop din kansa da kuma yadda zan yi amfani da lamarin.
Sai na fara tunani game da yadda zan dauki lamarin da gaske tare da tunanin hanyoyin da zan bunkasa harkar yadda zan buda wa wasu su ci abinci ta wannan hanya.
Haka kuma sai na fuskanci lamarin hip hop ya fi ci gaba a bangaren Kudancin kasar nan – a Kudu ne kadai suke girmama harkar nishadantarwa saboda suna da hanyoyin da suke yin hakan. Amma a Arewa ba su da rin wannan.
Hakan ya sa shekaru 10 da suka wuce sai muka fara yin wani shiri a Africa Magic Hausa muna yin wakokin hip hop.
Tun daga nan sai na kula cewa mutane sun fara karbar abin.
Daga baya kuma bayan Arewa24 ta zo sai suka ba ni dama inda muka kara bunkasa abin.
A yanzu kowa shaida ne game da yadda al’ummarmu ta karbi wannan harka ta waka.
A nan ne ma mutane suka fahimci cewa suna da basirar waka.
Wacce waka ce bakandamiyarka?
Gaskiya bakandamiya a wakokina suna da yawa domin ko wacce waka aka yi a lokacin sai in rika ganinta a matsayin bakandamiyata.
Lokacin da na yi “Ba su Feelings” na rika ganin ta a matsayin bakandamiyata.
Na zo na yi “Duniya Ina Za Mu Je”, wakar da ta yi tashe, har a gidan Rediyon Amurka sai da aka yi sharhin wakar.
Haka na zo na yi “Young Alhaji” ita ma na kasance ina ji da ita.
A yanzu haka ina da “Ya Rasulullah” wadda ita ma nake ji da ita.
Shi ya sa na ce miki babu wata waka da take bakandamiya a wurina.
Mene ne amfanin hip hop a rayuwar al’ummar Hausawa?
Hip hop hanya ce ta isar da sako. Za ka ga malami zai dade yana wa’azi amma ba a saurara; ko gwamnati tana da wani shiri amma mutane ba su fahimce shi ba, amma da zarar an yi amfani da wakar hip hop [sai a samu biyan bukata].
Hip hop ya samo asali ne daga bayi bakaken fata a Amurka.
A wancan lokaci wadannan bakake ba su da hanyar isar da sako a saurare su, don haka sai suka fara yin amfani da hip hop suna rubutu a bango suna zagin shugabannin Amurka, daga baya kuma suka fara waka.
A karkashin hip hop ba wai kawai waka ba ne, akwai zane-zane akwai DJ akwai MC da kuma uwa-uba abin da muke kira hip hop culture wato yin amfani da abubuwan hip hop, idan kika dauki T-Shirt da muke sanyawa harkar hip hop ce domin wadannan bakaken ne suka fara rubutu a jikin riga suna aika sakonni.
Wane kalubale kuke fuskanta
Babban kalubale a harkar ita ce ta satar fasaha.
Kana zaune ka yi aikinka wani zai je a gefe daya yana kwashe romon.
Akwai masu downloading da sauransu. Wannan yana daga cikin matsaolinmu wadanda muke fama kuma gwamnati ta sa hannu a ciki don nema mana mafita.
Duba da cewa kana gabatar da shirye-shiryen talabijin irin su “Zafafa Goma”, shin yanzu ka daina waka ne?
Ni ban daina waka ba. A takaice ma ni ba na yin wata uku ban yi waka ba.
A yanzu haka ma akwai album biyu da nake aiki a kansu wadanda muke yi da Osharey da Ricqy Ultra.
Ban da kuma aikina na kaina. Shi ya sa kullum nake cewa ai ni a cikin rudu nake.
Kuma kullum ina kokari kada na gaza, ina kokari na ba masoyana abin da suke so.
A kwanakin baya wani rubutu ya yi ta yawo a kafafen sada zumunta na zamani inda aka zarge ka da bata tarbiyyar yara. Me za ka ce a kan haka?
To a koyaushe nakan yi kira ga jama’a, musamman wadanda ba su fahimci abu ba, da su daina saurin yanke hukunci a kai.
Abu na biyu da zan fadi shi ne akwai mutane ’yan bakin ciki wadanda idan ba su suke yin abu ba to za su bata abin da baki.
Kun taba ganin wurin da aka hana nishadantarwa a duniya?
Ni kullum ina kalubalantar al’umma cewa su fito su bayyana wurin da yake bata tarbiyyar guda daya.
Mu fa muna da dokoki wadanda idan album din mawaki bai cika ba to ba za mu sanya wakarsa ba; idan bidiyo da batsa ko an yi shigar banza to ba mu sanyawa.
Sai mun tantance abin da ka fada a wakar ya dace da al’ummarmu sannan za mu sanya.
Abin da zan gaya miki kawai shi ne bakin ciki da wadansu ke yi, na je wani wuri da ba su je ba ko an san ni su ba a san su ba.
Duk wanda ke bin shirinmu na H Hip Hop inda muke kawo dan tsokaci a karshen shirin za ku ga fadakarwa ce a fakaice za mu ba ku labarai da zimmar nishadantarwa amma darasin rayuwa ne da yawa muke aike wa jama’a wadanda kuma daga yadda mutane ke mayar mana da martani mun san cewa suna karuwa da shi.
To ko ta nan mun fadakar. Alhamdulillahi.
Wadannan mutane suna kallon DSTV a gidajensu ba tare da tacewa ba.
Haka kuma wayoyi ne a hannun ’ya’yansu wadanda suke shiga intanet su kalli abin da suke so.
Duk ba su tsaya sun duba wannan ba sai abin da muke nunawa wanda kuma mu muke tantancewa tare da bin dokoki sau da kafa.
Wane sako kake da shi ga masoyanka?
Ina yi musu albishir cewa akwai ayyukan da muke yi a kasa da bidiyo da kuma album wadanda za su zo nan ba da dadewa ba.
Ina kuma yin amfani da wannan dama wajen yin kira ga duk mai wata fasaha ta hip hop, ba sai waka ba – kamar yadda na yi bayani a baya hip hop ya kunshi abubuwa da dama.
A kullum ina da burin na ga na ba duk wani mai fasaha gudummawa ta hanyar haskaka su yadda za a san da su a duniya.
Watakila daga nan su ma za su iya cin abinci ta wannan hanyar.
Ina kuma yin kira ga duk wani da yake ganin zai ba ni gudummawa ta yadda zan kara inganta abin to ina maraba da shi.