Shugaban kungiyar Jaddada Harkokin Siyasa da ci gaban Al’umma wacce a takaice ake kira DPM reshen Jihar Gombe, Malam Ibrahim H Kanku, ya ce suna goyon bayan matakan da Shugaban kasa Muhammadu Buhari yake dauka wajen yaki da cin hanci da rashawa.
Malam Kanku wanda ya yi furucin yayin da yake tattaunawa da Aminiya a Abuja, ya shawarci Shugaba Buhari ya kara kaimi don ceto kasar nan daga bala’in da cin hanci ya jefa ta.
“Ina mai tabbatar maka da cewa mun taru a nan Abuja ne don jaddada goyon bayanmu ga kokarin da Shugaban kasa Muhammdu Buhari yake yi na ganin ya kawo karshen cin hanci da rashawa a kasar nan. Kuma muna kira gare shi ya kara sanya himma ya ci gaba daukar matakan da suka dace kan yaki da cin hanci,” inji shi.
Ya bayyana takaicinsa dangane da yadda wasu shugabannin marasa kishi suka mayar da baitul malin kasar nan tamkar na kashin kansu.
Saboda haka sai ya shawarci shugaban ya sanya ido sosai wajen ganin hukumomin da lamarin ya shafa sun yi abin da ya dace wajen ganin an hukunta duk wanda aka samu da laifi.
Ya yi kira ga daukacin ’yan Najeriya su ci gaba da yin addu’a tare da bai wa shugaban goyon baya don cimma burin da ya sanya a gaba na ganin an hukunta duk wanda aka samu da laifi.
A karshe ya bayar da tabbacin cewa kungiyar za ta ci gaba da bayar da goyon baya tare da wayarwa da mutane kai a ciki da wajen Najeriya kan illar cin hanci da rashawa.
Muna goyon bayan Buhari kan yaki da cin-hanci – kungiyar DPM
Shugaban kungiyar Jaddada Harkokin Siyasa da ci gaban Al’umma wacce a takaice ake kira DPM reshen Jihar Gombe, Malam Ibrahim H Kanku, ya ce suna…