✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Muna fuskantar gurbatar muhalli’

Mazauna garuruwan da ke kusa da rukunin masana’antu na Chalawa a karamar Hukumar Kumbotso suna fuskantar gurbatar muhalli saboda yadda wasu masana’antu da ke yankin…

Mazauna garuruwan da ke kusa da rukunin masana’antu na Chalawa a karamar Hukumar Kumbotso suna fuskantar gurbatar muhalli saboda yadda wasu masana’antu da ke yankin ke fitar da wani dagwalo mai wari wanda kuma ya zamo barazana ga zamantakewar su.
Wani bincike da wakilinmu ya gudanar ya gano cewa al’umomin garuruwan Panshekara da Kai da Garu da kuma Zawaciki suna fama da warin wannan dagwalo da ke fita daga wasu kamfanonin jimar fata da kuma wani hayaki mai zafi da ke fita daga wasu manyan masana’antu, wanda wani lokacin dole ne mazauna wannan yanki suke rufe kofofinsu da tagogi domin kaucewa  illolin wannan  dagwalo da hayaki mai zafi ke  addabarsu  koda kuwa lokacin zafi ne.
Mafiya yawan mutanen da Aminiya ta zanta da su sun bayyana cewa suna cikin damuwa matuka kuma babu wani mataki da ake dauka wajen magance wannan matsala, inda suka yi kira da babbar murya ga karamar hukumar Kumbotso da ma’aikatar kula da muhalli ta Jihar Kano da kuma ma’aikatar lafiya da su dauki  mataki kan wannan al’amari domin kula da lafiyar al’umma.
Bugu da kari, wani wanda ya bukaci a boye sunansa, ya shaida wa wakilinmu cewa akwai wata masana’anta ta jimar fatu da kiraga da ke kusa da barikin ‘yan sandan da ke Chalawa, wadda take kwararar da wani dagwalo mai matukar wari, wanda dole ne su rufe kofofinsu domin kaucewa illolin wannan dagwalo, tare da fatan cewa za a dauki wani mataki na yin gyara a hanyoyin fitar  wannan dagwalo .
Sai  dai duk kokarin da Amniya ta yi na jin ta bakin jami’an kamfanonin ya ci tura saboda dukkaninsu sun ki yin wani bayani kan wannan batu. Hakazalika, wakilinmu ya yi kokarin jin ta bakin  jami’an karamar hukumar Kumbotso wadda ita ce masana’antun suke a yankinta, ya ci tura.