✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Muna bukatar addu’o’in samun galaba kan Boko Haram — Janar Abimbola

A yanzu yaki da ta’addanci ya kai matakin da sai an hada da addu’o’i.

Wani Babban soja a Najeriya, Birgediya Janar Abimbola Yussuph, ya bukaci da a rika yi wa dakarun sojin kasar addu’o’in samun nasara a yakin da suke fafatawa da Boko Haram da sauran ayyukan ta’addanci a fadin Najeriya.

Da yake amsa tambayoyin ’yan jarida a Abuja yayin taron addu’a karo na uku a wata majami’a a Abuja, ya ce a yanzu yaki da ta’addancin ya kai wani mataki da yake bukatar sai an hada da addu’o’i.

Ya ce: “Koda a yaki, akwai wani matakin da ake kai wa na lallai a bukaci addu’o’i saboda mutumin da yake fafata yakin yana da abin da ya yi imani da shi kuma ko mene ne abin ya kamata ka karfafa masa gwiwa domin ya ci gaba da yakin.

“Don haka muna bukatar taimakon addu’o’i domin ci gaba da yakin.

“Ina da yakinin da taimakon Allah za mu kawo kashen yakin, kasancewar a kowane yaki akwai lokacin da mutane za su ce lokaci ya yi da za a hau teburin sulhu.”