✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mun yi magana

Wani Badakkare ne ya je yawon neman karnuka a Arewacin Sakkwato. Ya kuwa dace ya samo, a kan hanyarsa ta komawa gida Zuru sai ya…

Wani Badakkare ne ya je yawon neman karnuka a Arewacin Sakkwato. Ya kuwa dace ya samo, a kan hanyarsa ta komawa gida Zuru sai ya bi ta wani garin Zamfarawa. Shi ne gardama ta shiga tsakaninsa da wani Bazamfare. Shi Badakkaren yake ce wa Bazamfare: ”Kai ko a Sakkwato da aka yi magana mun yi magana bare nan umu umu.” Bazamfare ya ce: “Can Sakkwato me aka ce maka? kai kuma me ka ce?” Badakkare ya ce: “Cewa aka yi ‘ku tafi daga nan!’ Mu kuma muka ce, mun tafi!”

Daga Abdulmajeed Umar Gumi, 08060322272