✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mun yi babban rashi —Iyayen matukin jirgin da ya yi hadari a Kaduna

Kawun daya daga cikin direbobin da suka rasu a hadarin jirgin saman soji a Kaduna, Abubakar Alkali ya ce sun yi babban rashin dan nasu.…

Kawun daya daga cikin direbobin da suka rasu a hadarin jirgin saman soji a Kaduna, Abubakar Alkali ya ce sun yi babban rashin dan nasu.

Kawun marigayin, Alhaji Sulaiman Dauda ya bayyana marigayin a matsayin jajirtaccen soja, wanda yake aiki tukuru wajen kare martabar kasarsa.

“Ya taso cikin rayuwa mai kyau. Muna cikin jimami matuka na rashin danmu.Sai dai mun yarda da kaddara, Allah Yake bayarwa, kuma Yake karba kasancewar mun taso ne cikin addini da imani da kaddara da tsoronSa,” inji shi.

Shi ma Birgediya Janar Umar Alkali, wanda wan marigayin ne ya ce duk da cewa sun ji zafin lamarin, amma sun yi amanna cewa duk mai rai mamaci ne.

“Ni ne wan Abubakar. Mahaifinmu ya rasu yana da shekara biyu. Don haka, ya taso ni ne a matsayin uba. Mun ji zafi matuka, amma sai dai mun san cewa duk mai rai mamaci ne,” inji shi.

A ranar Talata da ta gabata ce hafsoshin soja biyu suka rasu a hadarin jirgin sojin sama a Kaduna.

Majiya mai tushe ta ce matuka jirgin su biyu sun rasu ne a lokacin da suke samun horo a sansanin Sojin Sama da ke Kaduna.

Tuni aka yi jana’aizarsa a Barikin Sojan Sama na NAF Base da ke Kaduna kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

Har lokacin hada wannan labarin, Aminiya ba ta samu gano dayan direban da ya rasu ba, wanda ake tunanin dan koyo ne.

Hatsarin jirgin ya faru ne kimanin shekara daya bayan wani makamancinsa da ya Najeriya domin ta kafa binciken ritsa wasu manyan hafsojin sojin kasa a watan Mayun 2021 a Jihar Kaduna.

Hatsarin na 2021 shi ne ya kasance ajalin manyan hafsoshin sojin kasa 11, ciki har da Babban Hafsan Sojin Kasa na lokacin, marigayi Laftanar Janar Ibarhim Attahiru, a lokacin da suke kan hanyarsu ta halartar bikin yaye kuratan sojoji a Zariya.