Kungiyar Tarayyar Turai ta ce ta yanke duk wata hulda a kan abin da ya shafi tsaro tare da dakatar da duk wani tallafi na kudi da take bai wa Nijar, biyo bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a kasar.
Jagoran manufofin hulda da kasashe na Tarayyar Turai, Josep Borrell ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar.
- Tuna Baya: Tarihin Shugaban kasar Najeriya Alhaji Shehu Shagari
- NAJERIYA A YAU: Shin Da Gaske Gwamnatin Kano Na Shirin Dawo Da Sarki Sanusi II?
Wadanda suka yi wannan juyin Mulki na Nijar dai sun ayyana Janar Abdourahamane Tiani a matsayin shugaban kasa a ranar Juma’a, bayan da suka wancakalar da shugaba Mohamed Bazoum.
Tarayyar Turai, Amurka da sauran kasashen duniya sun yi kira da a saki shugaba Bazoum ba tare da gindaya wasu sharruda ba, kana a maido da Mulki dimokuradiyya a kasar.
Nijar ce kasar da ta fi samun tallafi daga kasashen yammacin Turai, kuma babbar abokiyar aikin Tarayyar Turai a wajen yaki da bakin haure da ke bi ta Sahara zuwa nahiyar Turai.
Bugu da kari, Tarayyar Turai tana da dakaru da ke aikin bada horo a Jamhuriyar Nijar.
Kungiyar Tarayyar Turai ta wallafa a shafinta na intanet cewa ta kasafta kudin da ya kai Yuro miliyan 503 tun daga shekarar 2021 don bunkasa sha’anin mulki da ilimi a Jamhuriyar Nijar.