✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mun shaida wa Tinubu illar fara yakin Nijar – Kabiru Gombe

Malamin ya ce Tinubu ya yi alkawarin gayyatarsu idan za a kuma taron ECOWAS

Fitaccen malamin addinin Musuluncin nan, Sheikh Kabiru Gombe, ya ce malaman kasar nan sun shaida wa Shugaban Kasa Bola Tinubu illar da take tattare da afka wa Jamhuriyar Nijar da yaki.

Ya ce a yayin ziyarar da suka kai wa Shugaban karkashin inuwar malamai ta Najeriya a cikin makon nan kan rikicin kasar Nijar, sun yi mishi gamsasshen bayani a kan lamarin.

Malamin, wanda kuma shi ne Sakataren Kungiyar Izala (JIBWIS) ta Najeriya, ya bayyana ne yayin da yake jawabi lokacin da suka ziyarci shugaban mulkin soja na Nijar, Abdulrahmane Tchiani a Yamai, babban birnin kasar.

Ya ce, “A cikin wannan tawagar tamu har da Farfesa Salisu Shehu, fitaccen malamin addini kuma shugaban Jami’ar Al-Istiqamah da ke Sumaila a Jihar Kano, wanda shi ne ya yi wa Shugaba Tinubu cikakken bayani a kan hatsarin yakin da ECOWAS ke shirin farawa a Nijar.

“A sakamakon gamsasshen jawabin da ya yi, ko da lokacin da aka ba shi ya yi jawabi ya kare, sai da Tinubu ya ce a kara masa har sai da ya kammala.

“Daga nan ne ya nuna godiyarsa bayan da ya ce ya gamsu da jawaban, sannan ya yi alkawarin idan za a kuma zaman shugabannin ECOWAS, zai gayyato si don su ma ya yi musu irin wannan jawabin domin su ma su fahimta,” in ji Kabiru Gombe.

A tsakiyar makon nan ne dai malaman suka ziyarci Shugaban Najeriya, Bola Tinubu, a fadarsa da ke Abuja, inda suka shaida masa kudurinsu na kokarin shiga tsakani domin warware dambarwar siyasar kasar ta Nijar.

Daga nan ne kuma suka bar Najeriya ranar Juma’a, inda a jiya kuma rahotanni suka tabbatar da cewa sun sami nasarar ganawa ido da ido da shugaban.

A baya dai, dukkan wani yunkuri na tattaunawa tsakanin wakilcin kungiyar Raya Tattalin Arzikin Kasashen Afirka ta Yamma (ECOWAS) da shugaban mulkin sojin na Nijar ya ci tura.

Sai dai a wannan karon, malaman na nuna cewa akwai alamun haske a ganawar tasu da shi.

Daga cikin malaman da suka halarci zaman akwai shugaban kungiyar Izala na Najeriya (JIBWIS), Sheikh Abdullahi Bala Lau da Shugaban darikar Kadiriyya na Afirka, Sheikh Karibullah Nasiru Kabara da wakilin Sheikh Dahiru Usman Bauchi, wato Sheikh Ibrahim Dahiru Bauci da wasu malaman da dama.