✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mun sha alwashin farfado da Kano Pillars – Babaganaru

Mai horar da ’yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars, Muhammad Babaganaru ya ce kungiyar tana daukar kyawawan matakai don farfadowa daga halin da…

Mai horar da ’yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars, Muhammad Babaganaru ya ce kungiyar tana daukar kyawawan matakai don farfadowa daga halin da ta shiga a makonnin da suka gabata, inda ya ba da tabbacin cewa da yardar Allah za su ci gaba da kokari don tabbatar da cewa kungiyar ta kasance zakara a gasar Firimiya ta bana.
Muhammad Babaganaru ya bayyana haka ne ga manema labarai a Kano, inda ya yaba wa magoya bayan kungiyar saboda yadda suke bayar da goyon baya bisa ladabi da kuma sanin ya kamata, kuma ya nuna jin dadinsa bisa yadda ’yan wasan sa suka buga wasa mai daukar hankali wanda hakan ya sanya suka samu nasara a kan kungiyar kwallon kafa ta Abia Warriors d aci 5-0.
Shugaban kungiyar Kano Pillars,  Alhaji Kabiru Baita ya shaida wa Aminiya cewa  tuni aka dauki kwararan matakai na inganta kungiyar kuma nan gaba kadan za a  kammala aikin bunkasa harkokin wasanni da sauran muhimman al’amura da suka wajaba don  ganin Kano Pillars ta zamo zakara a kakar wasanni ta bana.