Kamfanin Mai na Ƙasa (NNPCL), ya tabbatar da cewa ya sayi man fetur daga Matatar Dangote a kan Naira 898 kan kowace lita, ba Naira 760 ba.
Kamfanin ya ce sun tura sama da tanka 300 zuwa matatar, kuma sama da tanka 70, sun riga sun ɗauki man.
- Yadda Masarautar Kaltungo ke yakar yunwa da fatara — Mai Kaltungo
- Ba mu da hannu a kama Sowore — DSS
Ministan Kuɗi, Wale Edun, ya bayyana cewa NNPCL ne kaɗai zai rinƙa sayen man fetur daga Matatar Dangote, yayin da za a sayar da man dizal ga duk wanda ke da sha’awar saya.
Gwamnati ta amince da sayar da danyen mai ga matatun cikin gida da kuma sayan kayayyakin man fetur da kuɗin Naira.
Wannan mataki na da nufin rage matsin lamba a kan Naira, da kuma inganta samun kayayyakin man fetur a ƙasar nan.
Daga ranar 1 ga watan Oktoba, 2024, NNPCL za ta fara kai ɗanyen mai zuwa Matatar Dangote, wanda za a biya da Naira.
Gwamnati na kuma shirin kafa cibiyar hidima a Legas, wacce za ta haɗa hukumomin da ke kula da doka da tsaro don tabbatar da nasarar wannan shirin.