✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mun rayu kamar ’yan uwa da marigayi Sarkin Lafiya – Isyaku Ibrahim

Fitaccen dan siyasar nan Alhaji Isyaku Ibrahim ya ce sun yi rayuwa da marigayi Sarkin Lafiya Alhaji Isah Mustapha Agwai tamkar ’yan uwa na jini.…

Fitaccen dan siyasar nan Alhaji Isyaku Ibrahim ya ce sun yi rayuwa da marigayi Sarkin Lafiya Alhaji Isah Mustapha Agwai tamkar ’yan uwa na jini.

Alhaji Isyaku Ibrahim wanda Ibrahim dan asalin Karamar Hukumar Wamba da ke Jihar Nasarawa ne ya shaida wa Aminiya cewa ya san marigayi Sarkin ne tun suna matasa, inda ya ce: “Na kadu da jin rasuwar marigayi Sarkin Lafiya, Alhaji Isa Mustapha Agwai I domin na san shi ne tun lokacin da aka kai ni garin Lafiya daga garin Wamba don karatun Alkur’ani a tsakanin 1947 zuwa 1949. Ya girme min da shekara hudu, haka ta sa na dauke shi a matsayin yayana.”

Alhaji Isyaku Ibrahim ya ce “Marigayi Sarkin Lafiya mutum ne mai tsantseni, mai karmaci, mazan jiya ne wanda a kullum ya fi son jama’arsa fiye da kansa. Da ya zama Sarkin Lafiya, ina ziyartarsa a lokaci- lokaci domin in gashe shi. Sun yi aji daya da tsohon Babban Hafsan Sojojin Najeriya, Janar TY Danjuma a Kwalejin Gwamnati ta Katsina-Ala kuma har rasuwarsa suna abota matuka, shi ya sa ma TY Danjuma ya halarci jana’izarsa.  Lallai Jihar Nasarawa ta yi babbar rashi na Sarki kuma jagora. Wanda bai dauki kansa a matsayin babba ga sauran sarakunan jihar ba, duk da ya grime musu, ya yi uba da kuma kaka ga yawancinsu.”

Ya ce “Sarkin yana da halaye nagari da suka kamata jama’a su yi koyi da su, na farko shi ya na son a yi sulhu maimakon a ta da jijiyar wuya har a yi fada.”

Alhaji Isyaku Ibrahim ya ce, “Lallai Sarki Agwai ya kare mutanen Ibo lokacin yakin Biyafra. Ya kamata mutane su san cewa a garin Lafiya aka haifi Cif Jim Nwobodo da tsaohon Shugaban Majalisar Dattawa Joseph Wayas. Akwai wata  gona Zannura da ke Tudun Wadan Lafiya inda nan Ibo ke zuwa sayen kayan gona. Kuma mutanen Lafiya ’yan kasuwa ne, ba sa son kabilanci da musguna wa wani.

Mutane da yawa sun yi juyayin rashin Sarkin Lafiya Musulmi da Kirista da sauran jama’a baki daya.”

Dangane da tarihin Lafiya, Alhaji Isyaku Ibrahim ya ce “Lokacin da Lord Lugard ya zo yankin, ya kira taron sarakuna a garin Loko a 1918. Ya ce ya kira taron ne don ya sanar da mutane abin farin ciki don an gano kuza a garin Odege tun 1916. Kakana da mahiafina wanda yake da shekara 13 a lokacin sun halarci taron. Kuma a nan ne aka ba Sarkin Lafiya Abdullahi sandar sarauta.

“Ina kiran ga mutanen Jihar Nasarawa su san cewa mutane ne masu kasa mai dauke da arziki a karkashinta, amma ya dace a samu masu hazaka domin a ci albarkacin abin da ke binne a karkashin kasar don arziki ya wadata ga kowa a karkashin Gwamna Umaru Al-Makura da wadanda za su biyo bayansa, don a ciyar da jihar gaba,” inji shi.