✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mun rasa abubuwan ci gaba da yawa a Ajingi – Shugaba

Alhaji Hamisu Abdulhamid Ajingi, shi ne Shugaban karamar Hukumar Ajingi a Jihar Kano da bai wuce wata hudu da hawa kujerar ba, a tattaunawarsa da…

Alhaji Hamisu Abdulhamid Ajingi, shi ne Shugaban karamar Hukumar Ajingi a Jihar Kano da bai wuce wata hudu da hawa kujerar ba, a tattaunawarsa da Aminiya, ya bayyana karamar hukumar take fama da karancin kayan more rayuwa da rashin aikin yi a tsakanin matasa da kokarin da ya ce zai yi don kawo sauyi:

Rabilu Abubakar a Ajingi

Aminiya: Kasancewarka Shugaban karamar Hukumar Ajingi, mene ne kudurinka ga al’ummar yankin?
Hamisu Ajingi: A gaskiya mu al’ummar Ajingi muna da bukatu da yawa domin a lokacin ba ya akwai abubuwan ci gaba da muka rasa, kuma za mu yi dukkan mai yiwuwa wajen ganin mun samar da wadannan abubuwa na more rayuwa ga al’umma musamman samar da wutar lantarki da gina hanyoyi da taimaka wa bangaren lafiya. bangaren ilimi daga hawanmu mulki mun fara tabowa domin mun yi kwaskwarima ga wasu makarantun firamare mun bai wa daliban firamare da kananan sakandare Yunifom da takardun karatu kyauta ana kuma ba su abinci yadda ya kamata. bangaren lafiya muna da babbar matsala a babban asibitinmu ta rashin kwararru da manyan ma’aikatan jinya wanda hakan yake sa ana daukar marasa lafiya daga nan Ajingi a kai su Gaya. Amma alhamdulillahi yanzu mun fara shawo kan matsalolin inda na je na hada kai da hukumar masu yiwa kasa hidima ta Jihar Kano na roki a rika turo mana da masu digiri a fannin lafiya kuma an turo mana da likita daya da masanin harhada magunguna daya da zamansu a Ajingi yana taimakawa kwarai da gaske. Kuma don ganin kada su bijire daga baya yanzu muna biyansu alawus mai tsoka mun kuma samar musu da gida don kara musu kwarin gwiwa su zauna.
Aminiya: Su kuma matasa wane shiri kake da shi a kansu?
Hamisu Ajingi: Kamar makarantar koyon aikin jinya ta Kano da suke bayar da takardar shaidar karatu ta diploma da babbar diploma mun tura matasa don su yi wannan karatun kuma Ajingi tana daga cikin kananan hukumomi da aka dauki yaranta masu yawa, kuma hakan bai rasa nasaba da yadda muke bin sawun abubuwan da muke nema. Sannan dukkansu yaran muna ba su karfin gwiwar da zai sa su tsaya su yi karatu yadda ya kamata, kuma yanzu haka gwamnatin jiha karkashin Dokta Rabi’u Musa Kwankwaso za ta dauki ma’aikatan jinya dubu bakwai da 401, inda muke sa ran Ajingi za ta samu wani kaso a ciki, kuma hakan zai iya magance mana matsalar zaman kashe wando matasan ke yi saboda matasanmu wadanda suka gama karatun aikin jinya su fiye da dari ba su da aiki muka rike su muna ba su dan alawus da bai taka kara ya karya ba, don su taimaka wa yankinsu kafin irin wannan dama da muke sa rai ta samu.
Aminiya: Matasan da ba su yi karatu ba, akwai shirin da kuke yi ne don koya musu sana’o’i?
Hamisu Ajingi: Daga hawanmu karagar mulki gaskiya mun bai wa matasa da yawa jari a bangaren aikin noma domin akwai matasa da muka tura su koyi yadda ake yin huda da garmar shanu da yadda ake yin noma na tsawon mako shida, wanda idan suka koya muna ba su kudi su sayi shanu biyu da garma da amalanken shanu domin su dogara da kansu. Akwai wadanda muka tura suka koyi gyaran wayoyin hannu su ma muka ba su jarin da za su bude shaguna, sannan wasu mun tura su sun koyi aski irin na zamani wadanda duk mun ba su jarin sayan kayayyakin aiki yanzu duk sun dogara da kansu, kuma zaman kashe wando ya ragu sosai a cikin kankanen lokaci, kuma burina shi ne in ga nan gaba na bunkasa matasa kamar 500 kafin in sauka.
Aminiya: Zuwa yanzu matasa nawa ka taimaka mawa?
Hamisu Ajingi: Ka san duka-duka yanzu ba mu wuce wata hudu zuwa biyar da hawa wannan kujera ba, amma duk da haka na farfado da rayuwar matasa fiye da 50, inda yanzu haka suna nan sun zama masu dogaro da kansu kuma sun zama abin sha’awa a tsakanin al’umma. Kamar yadda na ce maka ina son in bunkasa matasa 500 yanzu haka na tura wa gwamnatin jiha batun har ta amince min da hakan saboda tsarin ya zo daidai da tsarin Gwamna Injiniya Rabi’u Kwankwaso, sai dai zan dauki abin kadan-kadan ne saboda yanayin kudi.
Aminiya: Mene ne kiranka ga al’ummar karamar hukumar?
Hamisu Ajingi: Kirana ga al’ummar Ajingi shi ne su ci gaba da yi mana addu’a ta fatan alheri don mu samu karfin gwiwar ci gaba da samar musu da ayyukan raya kasa da samun damar sauke nauyin da ke kanmu. Kuma jama’a su zama masu hakuri saboda halin rayuwa da ake ciki na rashin kudi wanda kowa ya sani, idan aka yi hakuri a hankali kowa zai shaida ribar mulkin siyasa.
Ga gwamnati kuma akwai wuraren da muke bukatar hanyoyi a wasu garuruwanmu da cikin garin Ajingi wadanda karamar hukuma ba za ta iya yin aikin hanya ba, sai gwamnatin jiha ta shigo, don haka muke roko gwamnati ta dube mu ta yi mana wadannan hanyoyi musammam hanyar Kunkurawa da hanyar da ta tashi daga Ajingi ta tafi Kadiri da hanyar Laraba da ta Kara idan aka yi mana su za su taimaka sosai wajen hada-hadar kasuwanci a tsakanin wadannan kauyuka namu.