✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mun lalata miyagun kwayoyi na N95bn a Kwatano – NAFDAC

An lalata kayan ne a birnin Kwatano na Jamhuriyar Benin

Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Kasa (NAFDAC) tare da hadin gwiwar gwamnatin Jamhuriyar Benin ta lalata kwantainonin Tramadol da sauran miyagun kwayoyi da kimarsu ta kai Naira biliyan 95.

Shugabar hukumar, Farfesa Mojisola Adeyeye ce ta bayyana hakan ranar Litinin a Abuja, lokacin da take yi wa manema labarai jawabi.

Ta ce kayan da aka lalata din wadanda aka haramta shigowa da su Najeriya ne sun hada da kwayoyin tamral (225 mg) da tamral (250 mg) da tramadol (120 mg) da tramadol (225mg) da Diclofenac (50 mg).

Ta ce tawagar tasu ta tafi har Kwatano, babban birnin kasar, inda aka lalata kwantainonin.

“Wannan nasarar da aka samu ta kasa da kasa wacce ba a taba samun irinta ba a tarihin kasashen biyu da NAFDAC, kuma ba ta samu ba sai da hadin gwiwar sashen bincikenmu da ke tashar jiragen ruwa ta Apapa da kuma kan iyakar Seme,” in ji ta.

Ta yi bayanin cewa an fara shirin gano kwayoyin ne daga wasu bayanan sirri da aka samu daga Fadar Shugaban Kasa a shekarar 2018, inda wasu bata-gari suka yi yunkurin shigo da kwantaina 31 na haramtattun kwayoyin daga Indiya.

Farfesa Mojisola ta ce an kunshe kwayoyin ne a matsayin kayan gini.

Ta ce an kawo kwantaina 21 a tashar jiragen ruwa da ke Apapa, inda guda biyu daga ciki ne kawai suke dauke da kayan ginin, daga bisani kuma aka karkatar da guda biyar zuwa Jamhuriyar ta Benin.

Ta kuma gode wa gwamnatin ta Benin da Ofishin Jakadancin Najeriya da ke kasar da Hukumar Kwastam da Hukumar Kula da Abinci da Magunguna ta Kasar Ghana kan irin rawar da suka taka wajen samun nasarar aikin.