✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mun kusan samun nasarar tilasta jami’an gwamnati sa ’ya’yansu a makarantun gwamnati – Mahuta

dan Majalisar Jihar Katsina Abdullahi Ibrahim Mahuta ya dade yana gwagwarmaya kan jami’an gwamnati sun mayar da ’ya’yansu makarantun gwamnati. A tattaunawarsa da wakiliyarmu, ya…

dan Majalisar Jihar Katsina Abdullahi Ibrahim Mahuta ya dade yana gwagwarmaya kan jami’an gwamnati sun mayar da ’ya’yansu makarantun gwamnati. A tattaunawarsa da wakiliyarmu, ya ce ga alama hakarsa ta yi kusan cimma ruwa, saboda yadda gwamnatin jiharsa ke kokarin rungumar shiri nasa da ya yi wa lakabi da ‘Ni Ma Na Yarda.’ Ga yadda tattaunawar ta kasance:

Aminiya: Kana kamfe din a koma karatu a makarantun gwamnati a takaice kai a in aka yi karatu?
Mahuta:  An haife ni a watan Afrilun 1970. Sannan na yi makarantar firamare ta Galadima na yi sakandare a makarantar Sakandaren Gwamnati da ke Malumfashi. Na yi Makarantar Kimiyya da kere-kere ta Katsina sannan na yi Jami’ar Abubakar Tafawa balewa da ke Bauchi da kuma Jami’ar Maiduguri, kuma duk na gwamnati ne.
A fanni aiki kuwa na dan taba aiki da wani kamfani mai zaman kansa kafin na bari na shiga harkar siyasa a shekarar 2011. Na tsaya takara kuma na ci zabe a matsayin dan Majalisar Jihar Katsina mai wakiltar karamar Hukumar Malumfashi zuwa 2015, yanzun kuma na sake komawa a bana. Allah Ya albarkace ni da mata biyu da ’ya’ya takwas.
Aminiya: Mene ne dalilin da ya sa ka shiga harkar siyasa?
Mahuta: Ina da imanin cewa ta hanyar siyasa ce kadai a yanayin dimokuradiyya da ake ciki yanzu mutum zai iya taimaka wa al’umma kamar yadda al’umma ta taimaka min ta hanyoyi da yawa har na kai na yi karatu, na samu ilimi mai inganci. Ta siyasa mutum na da dama da yawa inda zai iya taimaka wa wajen ganin al’umma ta inganta. Wannan biyan bashi ne tare da ba da tawa gudunmawar wajen raya al’umma.
Aminiya: Mene ne manufar shirin nan na “Ni Ma Na Yarda?”
Mahuta: Wani shiri ne da na kirkiro da nufin samo da doka da za ta tilasta wa duk wani ma’aikacin gwamnati da mai rike da mukami a gwamnati kan ya sa ’ya’yansa a makarantar gwamnati a jiharmu. Yin haka ne kadai nake ganin zai sa makarantun gwamnati su dawo da martabarsu ta da sannan a samu ingantaccen ilimi. Ma’aikata da masu rike da mukaman gwamnati su ke da alhakin inganta wadannan makarantu saboda haka dole ne su kawo ’ya’yansu wadannan makarantu da alhakin inganta su ya rataya a wuyansu. Kin ga ko ba komai, ke nan dole ne su yi abin da ya kamata albarkacin ’ya’yansu.
Dalili na biyu shi ne ganin a kawar da wariya tsakanin ’ya’yan masu tasowa inda ’ya’yan masu hali za su zauna daban da ’ya’yan marasa karfi alhali kuma duk al’umma daya ce. A ganina hakan bai dace ba don yakan haifar da mummunar wariya. Ana yanke zumunci tsakanin masu shi da marasa shi, tun ana kanana shi ya sa za ki ga wasu yaran sun taso babu tausayin wasu, ba su ki su buge su su kwace abin da ke hannunsu ba. Amma da an tashi tare, makaranta daya za a samu zumunta irin ta zamantakewa da za ta haifar da so da jin kan juna.
Aminiya: Wane irin kalubale kake fuskanta don ganin jama’a sun rungumi wannan shiri naka?
Mahuta: Mahatma Ghandi ya ce, “Ka zama mai ba da misali da kanka.” Don haka ne kafin in fito in fara wannan yekuwa na fara da kaina, inda na kwashi ’ya’yana na kai su makarantar gwamnati. Duk da cewa matata a lokacin ba ta yarda ba. Gaskiya a lokacin shawara ce da na yanke amma ba mai sauki ba ganin yadda makarantu gwamnati suka kasance, amma hanya daya ke nan kadai da zan iya jawo hankalin jama’a su san da gaske nake yi. In ba tare da yin hakan ba babu wanda zai fahimce ni sannan kuma na zama mai fadin abun da ni na kasa yi. Sannan na fuskanci kalubale daga wurin abokan hulda da na siyasa inda suka sa ni a gaba suna cewa ina amfani da ’ya’yana don siyasa wanda hakan a ganinsu ya yi tsauri da yawa. Su ana su sun dauka ina yi ne don siyasa a yayin da suka ga a zahiri ’ya’yana sun fara zuwa makarantar gwamnati.
kalubale na karshe shi ne su kansu yaran inda hakan ya shafi karatunsu da kuma rashin sabo da yanayin da suka samu kansu.
Aminiya: Wadanne nasarori wannan shirin ya samu?
Mahuta: Alhamdulillah bayan gwagwarmayar da muka shiga a kan wannan shiri na shekaru da dama a yanzu zan ce an samu gagarumar nasara tunda ya yi kusan zama tsari a Jihar Katsina, inda Gwamna Aminu Bello Masari ya yi alkawarin mayar da ’ya’yansa makarantar gwamnati, sannan duk wanda za a ba shi mukami a jihar Gwamnan ya ce dole sai ya mayar da ’ya’yansa makarantar gwamnati.
Na biyu kuma shi ne Majalisar Jihar Katsina ta bude zama don sauraron ra’ayin jama’a ko za a tilasa wa ma’aikatan gwamnati su sa ’ya’yansu a makarantun gwamnati. Abin shi ne, in dai makarantun gwamnati ba su dace da ’ya’yanka ba, to, lallai bai kamata aikin gwamnati ya dace da kai ba. Sai kai ma ka je ka samu aiki a wurin masu zaman kansu kamar yadda ’ya’yanka ke makaranta mai zaman kanta.
Aminiya: Menene fatanka ga wannan shiri na tilasta jami’an gwamnati su sa ’ya’yansu a makarantun gwamnati?
Mahuta: Fatana shi ne in ga cewa bai tsaya a Katsina kadai ba, amma ya shafi duk kasar nan baki daya kamar yadda kasar Malaysia ta mai da shi dole cewa jami’anta su kai ’ya’yansu makarantun gwannati, wanda hakan ya sa sun samu nasorori masu yawa a fannin ilimi. Tsohon Shugaba kasar Malaysia Dokta Mahathir Mohammed ne ya kawo tsarin inda ya zama dole ga duk ma’aikacin gwamnati ya kai ’ya’yansa makarantar gwamnati.