Kasar Rasha ta ce saura kiris ta kammala zagayen farko na abin da ta kira aikin da take yi a Ukraine, inda a yanzu za ta fi mayar da hankali wajen “ceto” yankin Donbas na Gabashin kasar.
Ma’aikatar Tsaron Rasha ta ce masu kokarin ballewa daga Ukraine da ke samun goyon bayanta a yanzu su ke iko da kaso 93 cikin 100 na yankin Luhansk da kuma kaso 54 cikin 100 na yankin Donetsk.
- An gano dan Minista Pantamin da aka sace a Bauchi
- 2023: Babu adalci a tsarin karba karba – Sheikh Jingir
Yankunan biyu dai su ne suka hadu suka yi yankin na Donbas da ke Gabashin Ukraine.
Shugaban sashen kula da ma’ikatan Rundunar Sojojin Rasha, Sergei Rudskoi, ya ce, “Mun yi matukar raunata karfin sojin Ukraine, wanda ya ba mu damar cika babban burinmu na ceto yankin Donbas.”
Ma’aikatar ta kuma ce akwai yiwuwar ta sake mamaye biranen Ukraine din da suka ki bayar da kai bori ya hau.
Rasha dai ta ce a shirye take ta mayar da martani ga duk wani yunkurin rufe wa jiragenta sararin samaniya saboda rikicin na Ukraine.
Tuni dai Ukraine ta nemi kungiyar kawancen tsaro ta NATO da ta rufe wa jiragen Rasha sararin samaniyar tasu, amma kungiyar ta ki.
Rasha dai ta sha alwashin ci gaba da hare-harenta a kan Ukraine din, har sai ta kammala ayyukan da Shugaba Vladimir Putin ya tsara yi a can, kodayake ba a bayyana su ba.