Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA) ta ce ta kama mutum 345 da take zargi da saye da kuma shan kwayoyin a Jihar Katsina daga farkon watan Janairun bana zuwa yanzu.
Kwamandan hukumar a Jihar, Mohammed Bashir, ne ya bayyana hakan yayin zantawarsa da manema labarai a Katsina ranar Litinin.
- Ana kokarin samar da fasahar da za ta sa masu kiba su rage kiba suna barci
- Ma’aikata sun yi zanga-zanga kan tsadar rayuwa a Landan
Ya kuma ce hukumar ta kuma sami nasarar gurfanar da 15 daga cikinsu a gaban kuliya.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya rawaito cewa taron dai na cikin jerin abubuwan da ake gudanarwa domin bikin Makon Yaki da Miyagun Kwayoyi na Majalisar Dinkin Duniya na 2022.
Taken bikin na bana dai shi ne: “Magance kalubalen lafiya da na ayyukan jinkai”.
A cewarsa, mutum 339 daga cikin 345 din da aka kama maza ne, guda shida kuma mata.
Ya ce sun yi wa akasarin mutum 338 din wa’azi kuma sun sauya hali, inda ya ce wasu daga cikinsu masu safara ne, wasu diloli wasu kuma masu sha ne.
“Ranar Yaki da miyagun Kwayoyi ta Majalisar Dinki Duniya ana yin ta ne a duk fadin duniya don wayar da kan mutane a kan illolin ta’ammali da miyagun kwayoyi da safarar su a cikin al’umma,” inji Kwamandan.
Ya ce wasu daga cikin abubuwan da za a yi yayin bikin sun hada da gasar kacici-kacici tsakanin makarantun sakandire na shiyyar mazabun Majalisar Dattawa uku na na yankin. (NAN)