✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Mun kafa kungiyarmu ne don mu yaki badala a Facebook’

kungiyar Mu Sada Zumunci  na Facebook da ke da hedkwatarta a birnin Kano ta ce an kafa kungiyar ne da nufin sadar da zumunci da…

kungiyar Mu Sada Zumunci  na Facebook da ke da hedkwatarta a birnin Kano ta ce an kafa kungiyar ne da nufin sadar da zumunci da kuma yaki da badala.
Shugaban kugiyar, Malam Nazeer Shatima shi ya bayyana haka a wani jawabi da ya yi kwanan baya, inda ya nuna cewa ’ya’yan kungiyar suna takaicin irin badalar da ake yi a facebook, lamarin da ya jaza yunkurin damarar yakarta, musamman da yake a halin da ake ciki suna da membobi mutum fiye da dubu biyar daga sassan kasar nan.
Shaharrarren dan wasan Hausa, Malam Kabiru Nakwango ya ja hankalin mahalarta taron muhimmancin yin zumunci don Allah kadai, domin duk zumuncin da aka kulla ba don Allah ba, karshensa nadama.
A nasa jawabin, uban kungiya, marubuci Alhaji Ado Ahmad Gidan Dabino ya ja hankali ne kan illar da kudi kan yi wa kungiya. “In ka ga kungiya na zaune lafiya, to ba ta da kudi, amma da zarar ta samu kudi, sai zargi da abubuwa marasa dadi su taso su kashe ta, don haka a yi hattara kar hakan ta samu wannan kungiya. kungiyoyin sadar da zumunci suna da muhimmanci, musamman a yau da duniya take dunkule”. Inji shi.