✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Mun kafa kungiyarmu ne don ci gaban matasan kasar nan’

Aminiya: Da farko za mu so ka gabatar da kanka? Alhaji Abdullahi: Sunana Alhaji Abdullahi Muhammed Nabayi shugaban kungiyar ’yan acaba da Keke Napep na…

Aminiya: Da farko za mu so ka gabatar da kanka?

Alhaji Abdullahi: Sunana Alhaji Abdullahi Muhammed Nabayi shugaban kungiyar ’yan acaba da Keke Napep na Jihar Bauchi na yi matukar farin ciki bisa wannan dama da kuka ba ni domin yin fashin baki game da yadda za a magance matsalar zaman kashe wando a tsakanin dimbin matasan Najeriya baki daya.
Aminiya: Yaushe kuka kafa wannan kungiyar?
Alhaji Abdullahi: Mun kafa wannan kungiyar ne a shekarar 2005 lokacin mulkin tsohon gwamnan Bauchi Alhaji Ahmed Adamu Mu’azu a shekarar 2009, amma tsohon gwamnan Bauchi Malam Isa Yuguda ne ya fara ba mu Keke Napep.
A shekarar 2013 aka zabeni a matsayin shugaban kungiyar, inda na karbi ragamar aiki daga wajen tsohon mai gidana, Alhaji Abubakar Adamu, wanda ya jagoranci kungiyar na tsawon shekara takwas.
Aminiya: Mambobin kungiyarku sun kai mutum nawa?
Alhaji Abdullahi: Muna da mambobi masu tuka Keke Napep a jihar nan fiye da mutum dubu uku. Kuma da yawa daga cikin wadanda suke wannan sana’a wasu sun gina gidaje, sun yi aure wasu kuma suna daukar nauyin iyayensu. Idan aka yi jimullah da ’yan acaba za a samu mutum dubu 28 da wani abu.
Duk fadin kasar nan, a Jihar Bauchi ne kadai mutum zai fito yana acaba tun daga karfe shida na safe har zuwa karfe biyu na dare babu wanda zai maka magana domin babu wata doka da ta takaita zirga-zirga.
Aminiya: Daga lokacin da ka karbi ragamar shugabancin wannan kungiya wasu nasarori aka samu?
Alhaji Abdullahi: Tabbas an samu gagarumin nasarori a shugabanci na farko na samu nasarori masu dimbin yawa daga wajen mambobin kungiyar kowa yana aikinsa tsakaninsa da Allah. Kuma muna shirya taron bita ga ‘yan acaba da keke daga lokaci zuwa lokaci ma’aikatar matasa da wasanni suna ba mu goyon bayan da ya kamata.
Aminiya: Za ka iya fada mana kadan daga cikin manufofin kafa wannan kungiya?
Alhaji Abdullahi: Kadan daga cikin manufofin wannnan kungiya shi ne tallafawa dimbim matasa wadanda suka yi rijista damu na biyu shi ne kungiyar tana ba da gudunmawa wajen koyawa matasa yadda ake kama kifi. Muna duka wadannan ne saboda idan matasa suka samu aikin yi a tsakanin al’umma tabbas za a samu raguwar aikata miyagun laifuka.
Aminiya: Me ya jawo wasu daga cikin ’yan acaba suka yi zanga-zanga a Bauchi kwanakin baya?
Alhaji Abdullahi: Tabbas akwai wasu daga cikin ’yan acaba wanda suka yi zanga-zanga har daga bisani suka fasa mana ofisoshinmu, amma mun sha kan matsalar kuma rundunar ’yan sandan jihar nan tana ci gaba da gudanar da bincike game da abin da ya faru nan ba da jimawa zamu sake yin jawabi ta kafofin watsa labarai.
Aminiya: Wane sako kake da shi ga mambobin kungiyarku?
Alhaji Abdullahi: Babban sakona ga mambobin wannan kungiya shi ne ya kamata a rika bin dokokin tuki. Kuma wanda suke sana’ar ba tare da rijista ba, su shafa wa kansu ruwa su yi rijista.
Sannan kuma muna kira da babbar murya ga ’yan acaba a guji daukar mutum biyu a lokaci daya duk wanda yasan ba ya da lamba a mashin dinsa, ya je ya saya tun kafin lokaci ya kure.
Ina rokon al’umma da su rika kawo mana rahotannin abubuwan da ke faruwa akan hanya. Mutane suna zarginmu da cewa mu azzalumai ne, amma Allah Ya san cewa muna iya bakin kokarinmu wajen sauke nauyin da aka dora mana.