Daliban Arewacin Najeriya sun janye daga shiga zanga-zangar gama-gari da ake shirin gudanarwa kan yunwa da tsadar rayuwa a kasar.
Daliban, karkashin gamayyar kungiyoyin dalibai masu kishin Arewa, sun sanar da janyewarsu ce ta wata wasika da Shugaban Majalisar Dattawa ta Kungiyar Daliban Jihar Kano ta Kasa (NAKS), Kwamred Jibrin Sani Bello.
Ya bayyana cewa sun yanke shawarar kaurace wa zanga-zangar ce saboda rashin sanin asalin wadanda suka shirya.
Kwamred Jibrin Sani Bello ya ce, “Shirye-shiryen zanga-zangar gama-garin sun riga sun yi nisa, amma bayan mun yi tuntuba da kuma zurfafa tunani, mun ga akwai buƙata daliban Najeriya sun kaurace wa zanga-zangar shiga ciki ta, da saboda rashin sanin wadanda suka shirya,” in ji shi.
Daliban sun bayyana cewa yawancin zanga-zangar da ake gudanarwa na kawo tsaiko ga harkokin karatunsu.
Sun bayyana cewa duk da yake matsalar tsadar rayuwa ta addabi ’yan Najeriya, akwai bukatar a yi hattara kada a kara tsananta lamarin ta hanyar zanga-zanga mara kyakkyawan tsari.
“Mun yard yunwa da tsadar rayuwa sun addabi ’yan Najeriya, amma duk da haka akwai bukatar a yi hattara da shiga zanga-zangar da ba a san asalinta ba, wadda kuma ba a san irin mummunan sakamakon sa za ta haifar ba,” in ji Kwamred.
Sun bayyana zargin an saye wadanda suka shirya, shi ya sa kungiyoyin suka yanke shawarar kauracewa.
Maimakon zanga-zangar muna kira da a fadada shirin ba da tallafin karatu ga dalibai (NELFIND) ta yadda za a rika daukar nauyin daliban da suka cancanta su yi karatu a cikin gida da kasashen waje,
Wani dalibi a Jami’ar Umaru Musa Yar’adua da ke Katsina, Abdulrahman Mansir, ya ba da misali da wasu lokuta a baya inda zanga-zanga ta sa aka tsawaita zangon karatu da birkita jadawalin karatun dalibai.
“Dole mu tsara kanmu a matsayinmu na dalibai, saboda zanga-zanga na iya kawo cikas ga ci gaban iliminmu kuma ba zai magance matsalolin Najeriya ba.
“Za mu koma ga Allah Ya magance mana matsalolin kasarmu,” in ji Mansur.