Idan har sauran gwamnoninmu na Arewacin Najeriya suka dauki irin matakin da Gwamna El-Rufa’i na Jihar Kaduna ya dauka za a tsaftace karatun makarantun Firamare a dukkan fadin kasar nan.
Sai dai ba a nan gizo ke sakar ba, wasu za su ga an yi rashin adalci na korar Malamai da yawa haka, ni ma da farko na kalubalanci abun, amma idan muka yi duba da idanun basira, za mu ga cewa ba wai fa wasu ake cutarwa ba fa, illa mu talakawa da ba mu da karfi ko galihun kai ‘ya’yayenmu makarantun kudi masu nagarta don samun Ilimin da muke ganin ana barinmu a baya idan muka hada kanmu da masu galihun
Wannan shi kadai ne yake cutar da mu rashi kwarewa ta musamman ga Malaman da ke koyar da yaran talakawa. Sai mu tambayi kanmu ko mene ne bambancin makarantun kudi da na gwamnatin?
Za ka isko albashin da ake biyan malaman makarantun kudi bai taka kara ya karya ba, amma kuma akwai kwarewa ta musamman da malaman suke da ita, akasin haka a na gwamnati me ya sa rashin kulawa da tabarbarewar Ilimi da rikon sakainar kashi da gwamnatin take yi wa bangaren ilimin muke ta hangowa ba kura-kurenmu a ciki ba.
Don Allah mu yi wa kanmu kiyamul laili, wallahi duk malamin makarantar da ke amsar albashin da ya haura dubu shabiyar Wallahi babu ‘ya’yansa a cikin makarantun da yake koyarwa sai dai ya kai su na na kudi.
Shawarata ga Gwamna El-Rufa’i da dukkan gwamnoninmu da za su dauki irin wannan matakin da su tabbatar da ba su fake da guzuma ba bare su harbi karsana, su yi don Allah don cigaban martabar farfado da ilimin yara ‘ya’yan talakawa kada su yi don cimma wata manufar siyasar su ko cutar da bayin Allah da ba su ji ba, ba su gani ba
Su tabbatar da ba su kori kowa aiki ba, su dai canza sabon zubi a makarantun ya’yan talakawa a yi #JUYIN-JUYA hali da dukkan wanda ba shi da kwarewar koyarwa a makarantun ‘ya’yan talakawa a tabbatar da adalci wajen tantancewa. Dukkan wanda ya dade yana karantarwar bai da kwarewar iya karantarwar a yi waje da shi. Wallahi muna goyan baya, ya yi daidai
A yi masa sauyi da wata makoma ta daidai da inda zai iya aiki ya amfani gwamnati ya amfani al’umma da sauyin aikin daidai da kwarewar shi.
Masu son zuwa karo ilimin koyarwa kuma a ba su dama suma su tafi su je su samu horo na karo ilimin iya koyarwa ta mu samman.
Idan aka tsaftace makarantun gwamnatin da kwararrun malamai wallahi ko a gindin itatuwa yaranmu ke zama suna karatu in a kwai malaman da suka cancanta su karantar za a samu sauyi mai nagarta da kuma yaye damuwar samun ilimin a saukake ba tare da damuwa ba. Za a wayi gari da samun ilimin ‘ya’yan talakawa da muka dade muna kukan ana cuta mana.
Sai an kai zuciya nesa da sa gaskiya da hikima ake gyaran iya tabbatar da sauke nauyin hakkin al’umma da ke kan shugabannin mu cikin adalchi.
Shugaban kungiyar Muryar Talaka Zamfara State Chapter <[email protected]> 07035304499