✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mun fi kowa iya aikin fata a kasar nan -Malam Sambo Madunka

Malam Sambo Madunka kwararren ma’aikacin fata ne a Jihar Sakkwato. Ya koyar da dimbin matasan jihar kan sana’ar, wadda kwarewarsa kan ta ta sa kowa…

Gamayyar kayayyakin fata da ake sakawaMalam Sambo Madunka kwararren ma’aikacin fata ne a Jihar Sakkwato. Ya koyar da dimbin matasan jihar kan sana’ar, wadda kwarewarsa kan ta ta sa kowa ya san shi. Aminiya ta tuntube shi kan haka, kuma ga yadda tattaunawar tasu ta kasance:

Aminiya: Mene ne tarihinka a takaice?
Malam Sambo: Sunana Malam Sambo Madunka, amma an fi sanina da Baba Sambo. Wannan sana’a nafi shekara arba’in ina gudanar da ita. Na koyar da mutane ita, ban san adadinsu ba. Kowane lokaci kana iya samun yara mata sun zo nan su karbi aiki da mai koyo da wanda ya iya.  A rana za ka iya samun wani ya samu Naira dari biyar zuwa kasa, don mukan yanka hoton doki ko tambarin Arewa ko wani abu daban, sai yaran su je su soke shi ga fatar da muka gyara. Mai gidana da ake kira Bawan Jalla shi ya fada min Sardauna ne ya tallafa wa wannan sana’ar tamu har ta kai inda take yanzu. Ya tura mutane Ingila suka koyo aikin fata suka zo suka koya mana. Sa’annan manyanmu na yanzu sun taimaka wajen habaka sana’armu don duk wani bako, kayan fata ne ake saya a ba shi a matsayin tsaraba. Sarkin musulmi ya taba sa muka yi wa Shugaba Gaddafi katuwar darduma. Ko kwanan nan da aka yi bikin Musulunci, bakin Larabawan da aka yi, kayan fata aka raba musu, kuma sun yi murna kwarai da gaske. Duk mu muka yi su. Ta haka ne Allah Ya daukaki wannan sana’ar tamu.
Aminiya: Mece ce alakar sana’ar fata da sunan unguwarku wato Madunka?
Malam Sambo: Abin da ya kawo haka a inda aka fito can da da hannu muke suka, kamar yadda ka ga ana sakar hula, to duk abin da ake suka a ja ana ce masa dunki shi ne ya sa ake kiranta Madunka, don a nan ne kadai za ka iya samun kushin da takalmi na fata da sauransu, wadanda aka yi da hannu. Duk wanda zai je unguwarmu sai ya ce bari ya je unguwar masu dunki. A nan ne ta samu sunanta na Madunka.
Aminiya: Shin duk mai sha’awar wannan sana’ar yana iya shigarta ko sai wanda ya gada?
Malam Sambo: Kowa yana iya shigarta don ko Gwamnan Sakkwato Magatakardan Wamakko ya sa mun koya wa wasu samari, maza da mata. Bayan lokacin da aka dibar musu ya kammala, sai ya raba musu teloli da kayan gudanar da sana’ar.
Aminiya: To yaya sana’ar take a zamanin da da kuma yanzu?
Malam Sambo: Sana’armu ba wani dogon bambanci da aka samu tsakanin lokaci da lokaci, domin dai kusan duk kayan aikin guda ne. Da farko muna aiki da fatar akuya da rago da shanu, amma duk fatar akuya ta fi kyau don ba ta kecewa, kana iya sarrafa ta yadda kake so, ko Turawa da ita suke amfani. Muna da kalar fata biyu: wadda muka gyara da wadda Turawa suka gyara, ta Turawan ta fi tamu kyau. A lokacin da muka fara, muna amfani da dankon zuma da dalkaki da hama da zare, amman a yanzu mun sami karin gam da buroshi da gol da zaren dinki da tela da kayan saka, ka ga bambancin ba mai yawa ba ne.
Aminiya: Wadanne abubuwa ne kuke yi da fatar idan kun sarrafa ta?
Malam Sambo: Kayan da muke yi da fatar Turawa, sun fi tsada fiye da tamu. Muna yin filo da darduma da bel na wando da titimai da takalma da huffi da rigar fata da safar hannu da hula da sauransu.
Aminiya: Yaya nasarori da kalubale fa?
Malam Sambo: Nasarar wannan sana’a ita ce ciyar da kaina da iyalina da nake cikinta. Sannan har cikin fadar shugaban kasa na shiga. Duk abin da rayuwa ke nema na samu, alhamdulillah! Matsalar kuma ita ce ta rashin tallafin gwamnati da kuma bashi da muke bi. A bikin kungiyar Musulunci da na fada maka, Gwamna Wamakko ya sa an karbi kayan miliyoyin Naira, kusan kowane shago sai da aka karbi kaya, amma har yanzu ba a biya ba. Ka ga ai wannan kokarin kashe mu ne, ba raya mu ba. Wallahi, a lokacin Bafarawa sana’ar ta fi kadari, don shi idan ya dauka yakan biya cikin lokaci sabanin yanzu. Wannan kusan ita ce kadai matsalarmu. Da an kawar da wannan, za mu kara bunkasa, don a duk fadin kasar nan ba wata jiha da ta kai nan iya sarrafa fata. Duk wasu kaya da ka gani a wani wuri, in dai ba na Sakkwato ba ne, sai ka ga bambanci, a dajiya ko wani abu daban. Mun fi kowa iya aikin fata a Nijeriya da za mu sami tallafin gwamnati da duniya ta kara tabbatar da hakan.