Hukumar Binciken Hatsari ta Najeriya (NSIB) ta fara bincike kan fashewar tankar man fetur da ya yi ajalin mutum 150 a Jihar Jigawa.
NSIB ta ce ta aike da ayarin ƙwararru domin gudanar da bincike da nufin gano ainihin musabbabin hatsarin da fashewar tankar man da ya yi ajalin mutane da dama.
Sanarwar da Daraktar Yaɗa Labaran hukumar, Bimbo Olawumi Olajide, ta fitar, ta ce bayan kammala binciken, ƙwarrarrun za su ba da shawarwari domin kauce wa aukuwar irin haka a nan gaba.
Lamarin ya faru ne a garin Majiya da ke Ƙaramar Hukumar Taura, sakamakon hatsarin tankar man fetur ɗin da misalin karfe 11 na dare ranar Talata.
- ’Ya’yana 4 da almajirai 5 sun rasu a gobarar tankar man Jigawa
- Boko Haram ta fille kan mutum 4 a Borno
Bayan faɗuwar motar da ke ɗauke da fetur daga Kano za ta kai Nguru a Jihar Jihar Yobe ne mazauna yankin Majiya da kewaye suka rika tururuwar zuwa kwalfar man da ke tsiyaya inda daga bisani wuta ta tashi.
Rundunar ’yan sandan Jihar Jigawa ta ce nan take mutane 94 suka ƙone har lahira wasu da dama kuma suka samu munanan raunuka.
Aƙalla mutane 125 ne aka yi jana’izarsu a ranar Laraba, a yayin da wasu sama da 75 suke kwance a asibitoci inda ake jinyar ƙunar da suka samu.
Jami’an ceto da likitoci dai sun bayyana fargabar cewa adadin mamatan zai iya ƙaruwa, duba da yanayin tsananin ƙunar da waɗanda ke kwance a asibitoci suka samu.