Babban Hafsan Sojin Najeriya, Janar Lucky Irabor, ya ce rundunar ta damka tubabbun ’yan ta’adda kimanin 613 masu saukin hatsari ga jihohinsu na asali.
Irabor, wanda ya bayyana hakan yayin taron wasu masu ruwa da tsaki na rundunar tsaro ta Operation Safe Corridor (OPSC) a Abuja ranar Alhamis, ya ce suna sa ran mutanen su fara sabuwar rayuwa a cikin al’ummominsu.
- Mutum miliyan 7 ne suka yi Umarah a 2022 – Saudiyya
- Hatsarin mota: Mutum 7 sun rasu a hanyarsu ta dawowa daga kamfen din Tinubu
Babban Hafsan, wanda babban jami’i mai kula da bayar da horo na rundunar, Manjo-Janar Adeyemi Yekini, ya ce yanzu haka mutum 613 suna can ana ba su horo domin canza musu hali.
Ya ce za a yi zuzzurafar tattaunawa da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, kan yadda za a gudanar da aikin sake shigar da su cikin al’ummar, gabanin a mika su ga jihohin nasu na asali.
Ya ce Buhari ne ya kafa rundunar ta OPSC a watan Satumban 2015 a matsayin wata dama ta yin afuwa ga ’yan ta’addan da suka tuba kuma suke so su ajiye makamansu.
Babban Hafsan ya kuma ce shirin afuwar wani aiki ne da ke gudana a karkashin hukumomi da ma’aikatun gwamnati daban-daban, kuma yake samun taimako daga daga kungiyoyi na gida da na ketare.