✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mun dakatar da jami’inmu kan zargin roƙon kuɗi — NIS

An dakatar da jami'in da ake magana a kai ba tare da wani ɓata lokaci ba har sai an samu sakamako na ladabtarwa.

Hukumar Kula da Shige da Fice ta Ƙasa (NIS) ta dakatar da Okpravero Ufuoma, wani Mataimakin Sufeto kan zargin roƙon kuɗi daga wani matafiyi.

Kwanturola Janar ta hukumar, Kemi Nandap ce ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, Mista Kenneth Udo ya fitar ranar Alhamis a Abuja.

Bidiyon da ya ɗauki jami’in yana roƙon kuɗi daga wani matafiyi a halin yanzu yana yawo a shafukan sada zumunta, mai taken “Haka jami’an shige da fice ke ɗaukar masu yawon buɗe ido a Najeriya.”

Yayin da take bayyana nadamar kan abin da jami’in ya aikata, Nandap ta ce, wannan rashin ɗa’a da aka ɗauka a wani faifan bidiyo da ke yawo a shafukan sada zumunta, ba ya nuna ɗabi’u da ƙa’idojin ƙwarewa da hukumar NIS ta yi.

“Wannan abin kunya ba ya nuna ƙwarewa da jajircewarmu na karɓar baƙi ballantana karramawa da kuma ladabi.

“Saboda haka, an dakatar da jami’in da ake magana a kai ba tare da wani ɓata lokaci ba har sai an samu sakamako na ladabtarwa,” in ji ta.

Nandap ta nanata ƙudurin NIS na ganowa tare da kawar da gurɓatattun jami’an da ke cikin muƙamanta da kawar dasu game da cin hanci da rashawa.