Hukumar NAPTIP mai yakar masu safarar bil’adama a Najeriya, ta sanar da samun nasarar ceto samari da ’yan mata fiye da 160 daga hannun miyagun mutanen da ke safarar ’yan Najeriya zuwa kasashen Libya da Italiya.
Wata kididdiga da ofishin shiyyar Kano na hukumar NAPTIP, wadda ta kunshi jihohin Kano, Kaduna, Katshina, Jigawa da jihar Bauchi, ta nuna an samu wannan nasarar ce daga watan Janairu zuwa makon jiya.
- Dan sanda ya mayar da N600,000 da aka tura masa bisa kuskure
- Za a yi itikafi bana a Masallatan Harami —Saudiyya
Bayanai sun fayyace cewa, matasan da galibin su sun fito daga shiyyar Kudu maso Yammacin Najeriya, jami’an na hukumar NAPTIP na samun kubutar da su ne bisa tallafin jami’an tsaro na jamhuriyar Nijar a kan iyakokin kasashen biyu.
Hakan dai na zuwa a dai-dai lokacin da hukumar ta NAPTIP ke fama da kalubalen kudade da na kayayyakin aiki.
Bayanai sun ce masu ruwa da tsaki da ke yakar masu safarar bil’adama a shiyyar Arewa maso Yammacin kasar sun koka game da karancin kudade da kayayyakin aiki daga gwamnati domin dakile ayyukan masu safarar mutane.
Sai dai, kungiyoyi masu zaman kansu na cikin gida wadanda ke aikace aikacen yaki da cin zarafin bil’adama da kuma safara da fataucin mutane sun ce sakaci da rashin kulawar gwamnati ne ya sanya batun yaki da masu safarar ’yan kasa ke samun koma baya.