Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta cafke wasu ’yan daba 13 da ake zargi da hannu a kone ofishin Barau Jibrin, Sanata mai wakiltar Kano ta Arewa da safiyar ranar Alhamis a Kano.
An rawaito cewar an cafke ’yan daban dauke da muggan makamai da miyagun kwayoyi.
- Bayan shekara 30, Kwalejin Ilimi ta yi bikin yaye dalibai a Gombe
- An gano gawar da ta shafe shekara 800 hannayenta na rufe da fuskarta
Kakakin ’yan sandanJjihar, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce tuni jami’an rundunar suka shawo kan lamarin, kuma an fara gudanar da bincike kan wanda aka cafke kafin mika su kotu.
“Yau 02/12/2022 da misalin karfe 8:00 na safe, mun samu rahoton wasu ’yan daba dauke da makamai sun farmaki ofishin Sanata Barau Jibrin, Sanata mai wakiltar Kano ta Arewa da ke kan titin Maiduguri a Kano.
“Bayan samun rahoton, Kwamishinan ’yan sanda CP Samaila Shu’aibu Dikko, ya tashi tawagar ‘Kan ka ce kwabo’ don tabbatar da tsaro a yankin tare da cafke wanda suka aikata laifin.
“Ba tare da bata lokaci ba tawagar ta bazama kuma ta yi nasarar cafke mutum 13 da ake zargin suna da hannu a lamarin. An same su da muggan makamai 34, gora 23, galan din fetur guda biyu, tabar wiwi, miyagun kwayoyi da sauran kayan maye,” a cewarsa.
Kakakin ya kuma ce Kwamishinan ’yan sandan Jihar, ya gargadi bata-gari cewar basu da maboya a Jihar, kuma duk wanda aka samu da laifi zai fuskanci fushin hukuma.