Sallama a gare ku Manyan gobe, tare da fatan alheri. A yau na kawo muku labarin ‘Mummunar Agwagwa’. Labarin ya na nuna mana cewa rashin dogoro ga halitta zai sanya mutum fadawa cikin mummunar hali. A sha karatu lafiya.
Taku: Amina Abdullahi
Akwai wata Agwagwa wadda take kwance akan kwan da ta yi guda goma sha biyu. A cikin wadannan kwayayen, akwai wani katon kwai wadda ta kasa fasawa. A hankali dai ta samu ta fasa sauran kwayayen ‘ya’yan agwagin suka fito.
Rannan sai ta ji kwan ya fashe pus! Sai ta ga wata katuwar mummunar agwagwa mai launin kore. Shikenan sai ta ce da ‘ya’yanta su je rafi su yi wanka daga nan zasu yawon neman abinci a kasuwa.
Suna cikin kasuwa sai mummunar cikinsu ta ga babu wadda ya damu da ita balle ya ba ta abinci. Yaran dake wasa da agwagi sai shurinta suke yi kamar kwallon kafa.
Wannan ya sanya ranta ta bace ta ce bari ta gudu ta fita daga cikin mutane kuma ta dauki alkawarin cewa ba za ta sake dawowa wajen mahaifiyarta ba.
Mummunar agwagwa ta yi ta gudu ba ta tsaya ba sai da ta isa wani daji wadda yake da kyawawan tsuntsaye a wannan dajin. Dajin ya kasance mai sanyi sannan kuma tsuntsayen wajen kyawawa ne.
Ba ta shiga daki domin dumama jikinta dangane da irin sanyin da ake yi ba. Ita a tunaninta, wai idan ta bar jikinta iska da sanyi suka hura ta sosai, tana ganin hakan zai sanya ta canza kamaninta zuwa kyakkyawa.
Kasancewar irin sanyin da ya yi ta bugunta sai ta shiga rashin lafiya mai tsanani wadda yasa aka nemi mahaifiyarta aka ba ta magani ta warke.
Tare da fatan Manyan gobe za su dauki darasi wajen godiya ga Allah ga irin halittar da Alla Ya mu su.