✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mummunan rikici ya kaure tsakanin makiyaya da manoma a Abuja

Akalla mutum uku ne suka jikkata a wani mummunan rikici da ya kaure tsakanin makiyaya da manoma mazauna Iddo, wata alkarya da ke Babban Birnin…

Akalla mutum uku ne suka jikkata a wani mummunan rikici da ya kaure tsakanin makiyaya da manoma mazauna Iddo, wata alkarya da ke Babban Birnin Tarayya na Abuja a ranar Litinin.

Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Abuja, ASP Mariam Yusuf ce ta ba da tabbacin hakan da cewa kura ta lafa a yayin da Kwamishinan ’Yan Sanda Ali Chiroma tuni ya jagoranci wani zaman sulhu tare da Shugabannin yankin na Iddo domin guje wa faruwar hakan a gaba.

Bukkoki da dama aka kona a yayin da mazauna yankin suka gwabza da Fulani makiyaya da ake zargi suna kada dabbobi kiwo a gonakinsu.

Sanarwar da ASP Mariam ta fitar ta ce, “Rundunar ’yan sandan Abuja ta samu nasarar kwantar da tarzomar da ta kunnu a garin Iddo biyo bayan rikicin makiyaya da manoma da ya barke tsakanin mazauna yankin a ranar Litinin.”

“Wannan mummunan lamari ya bar mutum uku cikin raunuka daban-daban baya ga wasu bukkoki da aka kona a yankin.”

“Kwamishinan ’Yan Sanda Bala Chiroma ya ba da umarnin gudanar da binciken diddigi a kan lamarin,” inji ASP Mariam.