✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mumbari ba wajen raddi da zage-zage ba ne — Sheikh Yusuf Langai

Zai fi kyau malamanmu su rika tabo kowane janibi na rayuwar al’umma.

Limamin Masallacin Masjidur Rahma da ke Tirwun a Jihar Bauchi, ya yi kira ga malaman addinin Musulunci su rika girmama mumbarin da Allah Ya ba su.

Ustaz Ishak Yusuf Langai ya ce malamai za su yi hakan ne ta hanyar karantar da jama’a tarbiyya da kyawawar karantarwar addinin Musulunci maimakon mayar da shi wurin mayar da martani da zage-zagen juna.

Ustaz Ishak Langai ya yi wannan kira ne yayin da yake tattaunawa da Aminiya a garin Kafanchan, inda ya jawo hankalin malaman su ji tsoron Allah, su sani Allah zai tambaye su nauyin da aka dora musu Ranar Kiyama.

“Musulunci bai rasa abin cewa a kowane janibi na rayuwar al’umma ba.

“Zai fi kyau malamanmu su rika tabo kowane janibi na rayuwar al’umma, musamman yankin Arewa da ake fuskantar matsaloli daban-daban kan rashin tsaro da lalacewar tarbiyya da yaduwar fasadi da talauci.

“Malamai na da gudunmawar da za su iya bayarwa ta hanyar karantar da al’umma hakikanin karantarwa da kuma fadakar da shugabanni nauyin da ke kansu don a gudu tare, a tsira tare,” in ji shi.

Ya ce, akwai fannoni na bunkasa tattalin arziki da aka yi wa Arewa nisa da ya kamata malamai su taimaka wajen fadakar da wadanda nauyin ya rataya a wuyansu, kama daga masu kudi da ’yan kasuwa zuwa ’yan siyasa da shugabanni da kuma kungiyoyi masu zaman kansu da ke tallafawa ta fuskoki daban-daban