Gwamnatin Jihar Kano ta sanya ranar Asabar 10 ga watan Yulin 2021 a matsayin ranar da za a tafka mukabala tsakanin Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara da malaman jihar Kano.
Kwamishinan Harkokin Addini Muhammad Tahar Adamu (Baba Impossible) ne ya bayyana haka yayin wata hira da Sashen Hausa na BBC da aka watsa ranar Alhamis.
- Bidiyon Dala: Kotu ta umarci Ganduje ya biya Jaafar Jaafar N800,000
- Ra’ayi: Yadda talla ke sanadin lalacewar ’ya’ya mata a Arewa
Ya ce za a gudanar da mukabalar ne a Hukumar Shari’a da ke birnin Kano.
Kwamishinan ya ce ya mika takardar gayyata ga malamin da sauran malaman da za su fafata a mukabalar.
Wannan na zuwa ne bayan zargin da Zauren Malaman Jihar Kano ya yi cewa gwamnatin Ganduje na bata lokaci wajen sanya ranar yin mukabalar.
Har wayau, a ranar Laraba wata babbar kotu a Jihar ta Kano ta saurari koken da lauyoyin Abduljabbar suka gabatar a kan hukuncin da wata kotun majistare ta yanje na rufe masa masallaci.
Damar kare kai
Alkalin kotun, Mai Shari’a Nura Sagir, shi ne ya bayar da umarni a gabatar da koken, bayan la’akari da korafin da malamin ya yi na rashin ba shi damar kare kansa daga zarge-zargen da ake yi masa.
Tun a ranar 4 ga watan Fabrairun 2021 gwamnatin Jihar Kano ta rufe masallacin Shaikh Abduljabbar tare da hana shi yin wa’azi bisa zargin yin batanci ga Sahabban Manzon Allah S.A.W.
Malamai da dama daga Kano da kewaye sun yi raddi a kan salon koyarwar malamin, inda suke ce ya saba da tsarin yadda ake koyarwa.
Sheikh Abduljabbar, wanda dan Darikar Kadiriyya ne, na sukar wasu Sahabbai da zarginsu da kirkirar Hadisai suna dangantawa ga Manzon Allah (SAW); yana kiran mabiyansa da su yi watsi da Hadisan.